An yi bikin daga tutar kasar Sin a filin Tiananmen don murnar cikar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin shekaru 77 da kafuwa a yau Alhamis 1 ga wata, a birnin Beijing.
Sojoji masu gadin tutar kasar, na rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin wato PLA, sun raka tutar zuwa filin Tiananmen, yayin da suke buga taken kasa.
Mutanen kasar Sin da dama ne suka kalli bikin zahiran a filin na Tiananmen.
Har ila yau, a kwanan nan ne ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen waje suka yi liyafa da sauran wasu bukukuwa, don murnar cikar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin shekaru 77 da kafuwa, inda manyan jami’an sassan kasa da kasa suka yaba da dimbin nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu, tare da bayyana fatan karfafa hadin gwiwa da kasar.
Frederick Shava, ministan inganta ilimin jami’o’i da kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, hadin gwiwar kasarsa da kasar Sin na taimakawa matuka ga bunkasar tattalin arzikin Zimbabwe, tare da kyautata rayuwar al’ummar kasar sosai. Ya ce Zimbabwe za ta ci gaba da bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kara kiyaye mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin a wurare daban-daban.
A nata bangaren, ministar kula da harkokin yawon bude ido ta kasar Afirka ta Kudu, Patricia De Lille, ta taya gwamnati gami da al’ummar kasar Sin murna a madadin gwamnatin kasarta, inda ta yaba sosai da nasarorin ci gaban kasar Sin, da gode mata saboda goyon-baya da taimakonta ga Afirka ta Kudu. Haka kuma, ta ce Afirka ta Kudu tana fatan kara habaka hadin gwiwa da mu’amala da kasar Sin, a wani kokari na ciyar da alakar kasashen biyu gaba. (Murtala Zhang)














