An gudanar da wani bikin nune-nunen hotuna a ranar Juma’a a Abuja, babban birnin Nijeriya, domin cika shekaru 81 da maido da Taiwan kasar Sin, inda ya samu halartar jami’an diflomasiyya, masana, shugabannin masana’antu, da kwararrun ‘yan jarida daga kasar Sin da Nijeriya.
Mai ba da shawara kan harkokin al’adu a ofishin jakadancin kasar Sin da ke Nijeriya, Yang Jianxing, ya bayyana cewa, dawo da Taiwan karkashin ikon kasar Sin wani muhimmin sakamako ne na nasarar da al’ummar kasar Sin suka samu a yakin da suka yi na turjiya ga mamayar kasar Japan, kuma hakan wani bangare ne na daukacin tarihin kasar Sin da ake tunawa da shi.
Yang ya ce, “Wannan bikin nune-nune ya kunshi tarin hotuna na tarihi masu daraja da kuma bayanai dalla-dalla a rubuce, wadanda ke nuna tsayin dakan al’ummar kasar Sin baki daya wajen riko da ka’idar ‘kasar Sin daya tak a duniya’ da kuma kare ‘yancin kai, hadin kai, da kuma martabar yankunan kasar.”
A nasa bangaren, shugaban Cibiyar Nazarin Alakar Sin da Afirka ta Zamani dake Nijeriya, Sheriff Ibrahim, ya bayyana cewa, Nijeriya na ci gaba da amincewa da ka’idar “Sin daya tak a duniya” kuma gwamnatin kasar tana ci gaba da jaddada wannan matsayi.
“Akwai kamanceceniya tsakanin kokarin da kasar Sin ke yi na kiyaye hadin kan kasa, da kuma irin abubuwan da Nijeriya ta karu da su wajen kiyaye martabar yankunanta,” kamar yadda Ibrahim ya bayyana, kana ya nuna kwarin gwiwar cewa, daga bisani dai kasar Sin za ta cimma burin sake hadewa da Taiwan cikin lumana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














