A yau Lahadi, kasar Sin ta harba rokar dakon kaya kirar Long March-8A daga tsibirin lardin Hainan na kudancin kasar, inda ta aike da wani rukuni na taurarin dan Adam na intanet zuwa sararin samaniya.
Rokar ta tashi ne da misalin karfe 10:03 na safe (agogon Beijing) daga cibiyar harba kumbuna ta kasuwanci da ke Hainan. Kayayyakin da aka yi dakonsu zuwa sama, wato rukuni na 28 na taurarin dan Adam na intanet da ke kusa da doron kasa, sun shiga da’irar da aka tsara zuwansu.
Cibiyar Ilimin Fasahar Sararin Samaniya na kasar Sin ce dai ta kera taurarin na dan Adam da aka harba.An kera rokar Long March-8A ne don cimma bukatun harba taurarin hanyoyin sadarwa a cikin da’irori masu matsakaicin nisa da kuma wadanda ke kusa da doron kasa.
Harba rokar ta yau, ita ce ta 674 a cikin jerin ayyukan harba rokar Long March mai dakon kaya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














