Daraktan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na yankin Yammacin Pacific, Saia Ma’u Piukala ya bayyana cewa, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen habaka ci gaban magungunan gargajiya a duniya, ta hanyar amfani da gogewarta wajen hade magungunan gargajiya da tsarin kiwon lafiya na gaba daya.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua dangane da babban taron duniya kan magungunan gargajiya na shekarar 2026, Piukala ya bayyana cewa, idan aka hade magungunan gargajiya da tsarin kiwon lafiya yadda ya kamata, magungunan gargajiyar za su iya inganta kyakkyawan sakamakon kiwon lafiya ta hanyar fadada damar samun ayyukan kiwon lafiya, musamman a matakin farko na kula da lafiya.
An gudanar da babban taron duniya kan magungunan gargajiya na shekarar 2026 ne a birnin Beijing, a ranakun 17 da 18 ga watan Oktoba.
A cewar Piukala, kasar Sin ta kafa tsarin magungunan gargajiya mai inganci wanda ya samu tallafi daga kakkarfan tsarin manufofi da kuma ci gaba da zuba jari a fannin ilimi da horaswa, bincike, samar da ayyukan hidimomi da iya tsara dokoki.
Kazalika, ya yi nuni da cewa, kwarewar da kasar Sin ta samu wajen hade magungunan gargajiya da tsarin kiwon lafiya a matakin farko da sauran ayyukan kiwon lafiya, yayin da take amfani da ka’idoji masu alaka da daidaita hadarin da za a fuskanta a bangaren magungunan da likitocin ba da magungunan gargajiyar ta dace kwarai da gaske, musamman da sauran kasashe na yankin Yammacin Pacific.
Haka nan ya ce, kokarin da kasar Sin ke yi na karfafa horas da kwararru, da tabbatar da inganci da kuma binciken kimiyya, shi ma yana ba da darussa masu alfanu domin inganta aminci da ingancin magungunan gargajiyar da kuma taimaka wa mutane yanke shawara mai kyau game da amfani da su. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














