ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

by Abubakar Sulaiman
3 hours ago
Tumatir

Farashin tumatir ya ci gaba da tashi a kasuwannin jihar Legas, duk da raguwar farashin barkono da ta ɗan sauƙaƙa wa ƴan kasuwa da masu sayayya.

Rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), ya nuna cewa tsadar tumatir na rage yawan cinikayya tare da ƙara wa iyalai kashe kuɗin sayen a kayan abinci.

Wani mai sayar da tumatir a tashar mota ta Costain, Malam Mohammed, ya ce farashin kwanon tumatir da a watan Agusta da Satumba yake ₦6,000 ya tashi zuwa ₦7,000. Haka kuma, farashin kwando ya ƙaru daga tsakanin ₦35,000 zuwa ₦40,000 zuwa tsakanin ₦45,000 da ₦65,000, gwargwadon iri da girman tumatir.

ADVERTISEMENT

Wata ƴar kasuwa, Rukayat Sherif, ta ce kwandon tumatir irin na Ghana yanzu yana tsakanin ₦40,000 da ₦45,000, yayin da a watan Agusta da Satumba ake sayar da shi kan ₦50,000 ko fiye. Ta ƙara da cewa farashin ƙaramin buhun Attaruhu ya sauka daga tsakanin ₦30,000 da ₦35,000 zuwa tsakanin ₦20,000 da ₦25,000.

Masu sayar da Attaruhu sun danganta sauƙin farashinsa da ƙaruwa da ake samu a kasuwa a wannan lokaci na kakar girbi. Sai dai sun bayyana cewa kuɗin sufuri da lodin kaya na ci gaba da shafar farashin da suke sayarwa. Wasu masu sayayya sun ce Attaruhu ya fi sauƙin samu a yanzu, lamarin da ke ba su damar sayen mai yawa da kuɗin da suke da shi.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

Mary Chigozie, wata mazauniyar Costain, ta ce tsadar tumatir ta tilasta mata rage yawan wanda take amfani da shi wajen girki, inda wasu lokuta take haɗa Attaruhu da tumatir ko kuma ta dafa miyar ja da man ja. Masu sayayya sun yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa manoma tare da samar da wuraren sarrafa kayan amfanin gona da adana su, domin rage ɓarnar abinci da kuma daidaita farashi a lokutan da kayan suka yi ƙaranci.

Tumatir
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola
  • Abubakar Sulaiman
    Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas
  • Abubakar Sulaiman
    EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

MASU ALAKA

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna
Labarai

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola
Labarai

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta  A Legas
Labarai

Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas

October 25, 2026
Next Post
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

LABARAI MASU NASABA

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

October 25, 2026
Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta  A Legas

Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas

October 25, 2026
An Yi Bikin Nune-nunen Hotuna A Nijeriya Bisa Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin

An Yi Bikin Nune-nunen Hotuna A Nijeriya Bisa Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin

October 25, 2026
EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.