Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun yi garkuwa da manoma biyu a ƙauyen Assako 1, da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, bayan sun kai hari a yankin da safiyar Lahadi.
Shugaban ƙauyen, Ali Na Allah, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Leadership, inda ya ce maharan sun shigo ƙauyen ne a kan babura tsakanin ƙarfe 9:00 da 10:00 na safe, sannan suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.
Harbe-harben sun jefa mazauna yankin cikin firgici, inda wasu suka tsere domin neman mafaka. Daga cikin waɗanda suka gudu akwai wasu masu ibada da ke halartar ibadar coci a lokacin da maharan suka shigo yankin.
Shugaban ƙauyen ya ce maharan sun yi awon gaba da manoman biyu daga gonarsu. Ya zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, ba a san inda suke ba, kuma babu wani bayani kan ko masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalansu ko sun buƙaci kuɗin fansa.
Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna bai yi nasara ba, domin mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba. Har yanzu ba a samu cikakken bayani kan matakan da jami’an tsaro suka ɗauka game da lamarin ba.














