ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, October 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

by Abubakar Sulaiman
2 hours ago

Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce za ta riƙa biyan mutanen da aka killace saboda ɓullar cutar Ebola tallafin ₦100,000 duk mako, domin taimaka musu wajen biyan buƙatun iyalansu da rage musu nauyin zaman killacewa.

Babban Daraktan NCDC, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026. Ya ce an ɗauki matakin ne bayan wasu daga cikin mutanen da aka gano sun yi mu’amala da mai cutar sun nuna damuwa kan kuɗin abinci, da masauki da kula da iyalansu yayin da suke ƙarƙashin sa ido.

Idris ya bayyana cewa tallafin na ₦100,000 ga kowane mutum a mako wani mataki ne na gaggawa da ba a tsara tun farko ba, amma ya zama dole domin sauƙaƙa wa mutanen bin umarnin hukumomin lafiya. Ya ce za a ci gaba da duba yadda tsarin zai gudana bisa halin da ake ciki.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta zo ne yayin da adadin mutanen da ake sa ido a kansu bayan tabbatar da ɓullar cutar Ebola ta nau’in Bundibugyo a Nijeriya ya ƙaru daga 44 zuwa 53. Mutanen sun haɗa da ma’aikatan lafiya, da ma’aikatan gida da wasu da suka yi mu’amala da matar da aka tabbatar ta kamu da cutar bayan ta dawo daga Uganda.

Babban daraktan ya kuma jaddada cewa alhakin shawo kan irin wannan annoba bai kamata ya rataya a wuyan Babban Birnin Tarayya Abuja kaɗai ba.

LABARAI MASU NASABA

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Ya buƙaci gwamnatocin jihohi su tanadi kuɗi da kayan aikin da ake buƙata domin gudanar da aikin gano waɗanda suka yi mu’amala da masu cutar, killace waɗanda suka dace da kuma hana yaɗuwar cutar.

Hukumar ta kuma buƙaci jama’a su ba jami’an lafiya haɗin kai tare da dogaro da sahihan bayanai.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas
  • Abubakar Sulaiman
    Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas
  • Abubakar Sulaiman
    EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

MASU ALAKA

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna
Labarai

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas
Labarai

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta  A Legas
Labarai

Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas

October 25, 2026
Next Post
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

Xi Da Sarki Philippe Na Belgium Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 55 Da Kulla Alakar Kasashensu

October 25, 2026
Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

Mai Taimaka Wa Babban Sakataren MDD Ya Yaba wa Kasar Sin Bisa Hangen Nesanta

October 25, 2026
Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma  2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Manoma 2 A Wani Sabon Hari A Kaduna

October 25, 2026
NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

NCDC Za Ta Fara Biyan Mutanen Da Aka Killace ₦100,000 Saboda Ebola

October 25, 2026
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Na Intanet

October 25, 2026
Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

Farashin Tumatir Ya Tsiri, Na Barkono Ya Sauka A Legas

October 25, 2026
Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

Jami’in WHO: Kasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Habaka Ci Gaban Magungunan Gargajiya A Duniya

October 25, 2026
Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta  A Legas

Hatsarin Manyan Motoci Biyu Ya Hallaka Uwa Da Ɗanta A Legas

October 25, 2026
An Yi Bikin Nune-nunen Hotuna A Nijeriya Bisa Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin

An Yi Bikin Nune-nunen Hotuna A Nijeriya Bisa Cika Shekaru 81 Da Maido Da Taiwan Kasar Sin

October 25, 2026
EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

EFCC Ta Buɗe Shafin Ɗaukar Ma’aikata Na 2026, Duba Sharuɗɗan Neman Aikin

October 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.