Connect with us

KASASHEN WAJE

Ana Ci Gaba Da Zanga-zanga A Kan Yadda Ake Tsare ‘Yan Cirani A Amurka

Published

on

Ana ci gaba da zanga zanga a jihar Tedas saboda yadda aka tsare bakin haure da aka raba da ‘ya’yansu kuma har yanzu babu wata hanya kwakwara da zasu sake haduwa da ‘ya’yansu cikin sauki.
To a nan Amurka ma, ana ci gaba da zanga zanga kan yadda ake tafiyar da ‘yan ciranin da aka tsare a jihar Tedas, wadanda suka shiga kasar ba bisa ka’ida ba, duk da cewa a ranar Laraba gwamnatin shugaba Trump ta sauya tsarin da take amfani da shi na raba ‘ya’ya da iyayensu a kan iyakar kasar.
A jiya Lahadi, jami’an tsaron kan iyaka suka saki kimanin iyaye 30 da aka raba da ‘ya’yansu, an kuma fasa tuhumarsu saboda dokar da suka karya ta shiga kasar ba tare da izini ba.
Darektan kungiyar Annunciation da ke tallafawa bakin hauren, Ruben Garcia, ya ce, zabin da aka baiwa bakin hauren kan yadda za su samu bayanai game da ‘ya’yansu, bai taka kara ya karya ba, domin an ba su lambar 8-0-0 ce kawai domin tuntubar halin da suke ciki.
Wasu daga cikin iyayen, an tsare su ne a wani wuri da ke karamar hukumar El Paso a cewar Garcia

Advertisement

labarai