Wata mata mai shekaru 43, da aka bayyana sunan ta da Funke Benson, wacce ake zargi da satar kusan kilo 23.8 na sarkar gwal da abin hannu wanda kudinsa ya kai Naira 597,000, a ranar Laraba ta bayyana a gaban wata Kotun Majistare da ke Surulere na Jihar Legas.
‘Yan sanda sun tuhumi Benson, wacce ake zargi da laifuka biyu na hadin baki da sata.
Mai gabatar da kara na ‘yan sanda, sufeto Courage Ekhueorohan, ya fadawa kotu cewa, wacce ake kara tare da dan uwan ta da ya gudu, sun aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Janairu, a Kasuwar Tejuosho, Yaba da ke Jihar Legas.
Ekhueorohan ya yi zargin cewa, wacce ake karar, wacce ke tare da wani mutum, ta shiga shagon Abubakar Ali, don sayen sarkar gwal, a inda ba zako ba tsammani, suka lacce shi
Mai gabatar da kara ya gabatar da cewa, yayin da wacce ake kara da abokin aikin na ta ke cinikin sarkar gwal, sai mutumin (shi abokin aikin na ta) ya nemi fita don yi fitsari, dawowar da bai yi ba kenna shagon Ali.
Ya ce, lokacin da Ali (mai shigar da kara) ya lura da sarkar gwal da abin hannu sun bata, sai ya tambayi wacce ake kara, a inda ta musanta cewa ba ta dauka ba. An tsare wacce ake kara a shagon, yayin da Ali ya kira ‘yan sanda.
Laifin, in ji shi, ya ci karo da sashi na 287 da 411 na dokar aikata manyan laifuka ta jihar Legas, ta shekarar 2015.
Benson, ta musanta aikata laifin.
Alkalin kotun M.I. Dan-Oni ya bayar da belin wacce ake kara a kan kudi Naira 200, 000 tare da mutane biyu wadanda za su tsaya ma ta.
Alkalin ta dage sauraron karar har sai ranar 3 ga watan Fabrairu, domin ci gaba da shari’a.