Kamar yadda aka shaida a 2013, lokacin da hadakar jam’iyyun siyasa da fusatattun mambobin na jam’iyya mai mulki ta PDP, lokacin da suka hadu suka kafa jam’iyyar APC tare da kayar da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da jam’iyyarsa a zaben 2015.
Saboda haka, gabanin zaben 2027, irin wannan al’amarin yana faru tare da ‘yan siyasa da aka fusata da kuma wadanda ke jin haushi a cikin APC, da shugabannin jam’iyyar adawa sun mika takardunsu ga hukumar zaben mai zaman kanta kasa (INEC) don kafa hadakan jam’iyya ta ADA don hambarar da APC.
- Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 1,191, Sun Ceto 543 Cikin Watanni Uku
- Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami
Shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda shi ma yana daga cikin mamba a cikin hadakar a 2013, wanda daga bisani aka samar da APC, kuma har ya kawo karshen mulkin PDP, shin ko shugabannin adawa sun shirya amfani da irin wannan dabarar don kwace mulki a 2027?.
Bisa yadda aka fara gwagwarmayan zaben 2027 a cikin hanzari, Tinubu bai da lokacin batawa wajen fitar da lissafin siyasarsa lokacin da aka samu labarin murabus din shugaban jam’iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje a ranar Jumma’a. Murabus dinsa na bazata ya haifar da rudani da saka alaman tambaya ga sakateriyar jam’iyyar ta kasa.
Tsohon gwamnan Jihar Kano ya mika takardar ajiye aiki ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar a ranar Juma’a, yana mai bayyana dalilansa na rashin lafiya.
Tun daga lokacin da ya yi murabus, ana ta bayar da dalilai da dama kan aje mukaminsa na bazata. Yayin da wasu ke cewa lamarin zanga-zangar da aka yi a taron masu ruwa da tsaki na APC a yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar a Jihar Gombe game da rashin jaddada sunan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima na goyon bayan tazarcen Tinubu a 2027, wasu kuwa sun ce zargin cin hanci da rashawa ake masa shi ne abin da ya kawo karshen mukaminsa.
Yayin da wasu suka yi tunanin cewa duk da zanga-zangar da mambobin jam’iyyar suka yi a sakateriyar jam’iyyar na kasa, an zargi Ganduje da yin amfani da masu sauya sheka da ke shiga jam’iyyar wajen sauya tsarin jam’iyyar.
Wasu na ganin mai yiwuwa saboda dawowar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Kwankwaso ya taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar shugaban na fitar da Ganduje ta hanyar yin murabus.
Masu sharhi kan al’amurar siyasa na ganin cewa idan har dai Ganduje na matsayin shugaban APC, zai yi matukar wuya Kwankwaso ya koma cikin jam’iyyar, saboda yadda ake takun saka tsakanin Ganduje da Kwankwaso, sannan kuma Tinubu ya dade yana zawarcin Kwankwaso wajen shigowa APC. Sun kara da cewa kan wannan tunanin ne aka yi zaton cewa barin Ganduje wani yunkuri ne na musamman don saukaka hanyan komawar Kwankwaso zuwa APC, wanda zai iya rage adawa a arewa da kuma karfafa Tinubu a 2027.
A cewarsu, a fili yake, daga cikin manyan matakin siyasar da Tinubu ya dauka domin sharar fage na tunkarar zaben 2027 shi ne, saita hanyar da za ta bulle masa zuwa 2027. Misali, a ranar Alhamis da ta gabata, shugaban ya tabbatar da sulhu tsakanin Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, duk suna nuni da wani lissafin Tinubu na kara karfi a dukkan bangarorin Nijeriya.
Tare da ficewar Ganduje, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga yankin arewa ta tsakiya ba su bata lokaci ba wajen sabunta kiransu na samun kujerar shugabancin jam’iyyar na kasa.
Tun lokacin da aka kafa APC a 2013, APC ta yi shugabanni guda shida da suka hada da Cif Bisi Akande (2013 zuwa 2014), Cif John Odigie-Oyegun (2014 zuwa 2018), Kwamared Adams Oshiomhole (2018 zuwa 2020), Mai Mala Buni (2020 zuwa 2022), Sanata Abdullahi Adamu (2022 zuwa 2023) da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje (2023 zuwa 2025).
Matakin Tinubu na sadaukar da Ganduje don dakile barazanar shugabannin adawa kafin zaben 2027 zai kara shaida ga wadanda suke da shakka cewa Tinubu har yanzu yana da kwarewa a cikin harkokin. Lokaci ne kadai zai tabbatar da babuwan da zai faru a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp