APC Ta Dakatar Da Shugaban AMAC Bisa Zargin Cin Amanar

APC

Daga Yusuf Shuaibu

 

Jam’iyyar APC a gundumar Jiwa da ke babban birnan tarayya ta dakatar da shugaban karamar hukumar Abuja ta tsakiya, Honourable Abdullahi Adamu Candido bisa zarginsa da cin amanar jam’iyya da kuma janyo rikici wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC na shekarar 2014 wanda aka yi wa kwaskwarima.

A cikin wasikar dakatarwar daga jam’iyyar wanda shugabannin gundumar suka rattaba hannu da aka gabatar wa manema labarai, ta bayyana cewa, “karkashin shafi na 21na dunkin tsarin mulki na jam’iyyar APC na shekarar 2014 wanda aka yi wa kwaskwarima, an lissafo mambobin zantarwa na jam’iyyar APC da ke gudumar Jiwa wadanda suka bayar da sanarwa a gare ka na cewa, mu ba mu da tabbaci a kanka a matsayin mambar jam’iyyar APC, sakamakon cin amanar jam’iyya da karya dokokin tsarin jam’iyyar.”

Haka kuma jam’iyyar ta zargi Candido da hada kai da shugaban karamar hukumar Jiwa, Alh. Bala Madaki wajen kawo barazana ga mambobin zantarwa na garin Jiwa ga duk wanda ya ki goyan bayansa, sannan ya hada kai da shi wajen gudanar da zanga-zanga na rikici a kan matakin da uwar jam’iyya ta dauka. A cewar jam’iyyar, a lokuta da dama, Candido yana bayar da bayanai na karya a kan zaban fidda gwanin da jam’iyyar ta samu nasarar kammala cikin nasara, domin janyo kiyayya a zukatar ‘ya’ayan jam’iyyar tare da gudanar da taruka daban-daban da jam’iyyun adawa.

Wasikar ta kara da cewa, “ka gudanar da abubuwa wanda suka saba wa dokokin jam’yyar APC, sannan kana fusata ‘ya’yan jam’iyyarmu a cikin kalamun da ke gabatarwa.

“Muna sane da cewa ka gudanar da taruka da dama domin bayar da mugayan bayanai ga jam’iyya mai mulki, wanda hakan ya janyo kiyayya a zukatan ‘ya’yan jam’iyya.

“Saboda haka, karkashin sashi na 21 na dokokin jam’iyyar, mu shugabannin zantarwa na jam’iyyar APC na gundumar Jiwa, mun dakatar da Hon Abdullahi Adamu Candido bisa rashin ladabi da cin amanar jam’iyya da saba wa dokokin jam’iyyar APC,” in ji jam’iyyar.

Wani majiya wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana wa manema labarai cewa, shugaban karamar hukumar ya yi kokarin bai wa shugabannin zantarwar cin hancin naira 200,000 ga kowannan su domin su goyi bayan burinsa na kashin kai.

Hakazalika, a gundumar Karshi jam’iyyar APC ta dakatar da Hon. Hashimu Suleiman Angama bisa zargin cin amanar jam’iyya da takardun karya da karya dokokin tsarin jam’iyyar APC na shekarar 2014 da aka yi wa kwaskwarima. A cikin wasikar shugabannin zantarwar jam’iyyar a kan takarar da Angana ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2021 ta ce, “karkashin shafi na 21na dokokin tsarin mulkin jam’iyyar APC na shekarar 2014 Wanda aka yi wa garanbawul, mu mambobin majalisar zantarwa na gundumar Karshi muna sanar da kai cewa ba mu da tabbaci a kan ka bisa cin amanar jam’iyya da saba wa dokokin jam’iyyamu.

“Ka kasa gudanar da bayanai masu karfi da zai hada kan mambobin zantarwa na gundumar Karshi, dukkan bayananka suna wargaza hadin kan ‘ya’yan jam’iyyarmu wadanda suke janyo kiyayya tun daga gundumar zuwa karamar hukumar da kuma mataki ta jiha ba tare da la’akari da matsayin da kake rike da shi a cikin jihar ba,” in ji ta.

Haka kuma, jam’iyyar tana zargin Angana da daukan kansa a matsayin mai zantarwa shi kadai, wanda yake zantar da hukunci a kan al’amura ba tare da bin ka’idojin jam’iyyar ba duk da akwai shugaba a cikin gundumar.

“A ganinka kana iya cire wadanda ka ga dama a cikin mambobin zantarwa da wadanda aka zaba ba tare da bin ka’idojin da dokokin tsarin jam’iyya ta shardanta ba.

“Matakin da ka dauka na yin amfani da jabun takardun makaranta sun saba wa tsarin jam’iyyar wanda ya janyo dakatar da kai daga tsayawa takarar a zaban fidda gwani na shugaban karamar hukuma a garin Abuja.

“Saboda haka, mun rattaba hannun a matsayinmu na mambobin zantarwa na jam’iyyar APC a gundumar Karshi na takatar da Hashimu Suleiman Angama daga cikin jam’iyyar, bisa kwararan hujjoji da muka samu a kanka.

“Takatarwar ta zo ne bayan kammala zaban raba gardama a kan ka wanda yake kunshe a cikin wata wasika na ranar 30 ga watan Junairun shekarar 2021, wanda mambobin zantarwa guda 24 na garin Karshi suka rattaba hannu da aka gabatar wa shugaban gundumar Karshi,” in ji jam’iyyar.

Haka kuma, a gundumar Jiwa jam’iyyar APC ta dakatar da shugaban karamar hukumar mai suna, Alh. Bala Madaki daga jam’iyyar, bisa saba wa dokokin tsarin jam’iyyar APC na shekarar 2014 wanda aka yi wa kwaskwarima. An takatar da shi ne a cikin wata wasika na ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2021, wanda shugabannin zantarwa na jam’iyyar suka rattaba hannu.

Wasikar ta ce, “karkashin shafi na 21 na tsarin dokokin jam’iyyar APC na shekarar 2014 wanda aka yi wa garanbawul, mu mambobin zantarwa na jam’iyyar APC a gundumar Jiwa muna sanar maka da cewa ba mu da tabbaci a kan ka a matsayin mambar jam’iyyar APC sakamakon karya tsarin dokokin jam’iyyar.

“Takatarwar ta zo ne sakamakon kin gurfana a gaban kwamitin bincike da aka kafa na zargin da ake yi maka a lokuta da dama.

“Kai tsare kana yin barazana a fili da bayyana wa wasu mambobin zantarwa domin sun ki bin goyan bayanka. Ka hada kai da shugaban karamar hukumar Abuja ta tsakiyar wajen shirya zanga-zangan tayar da rikici bisa hukuncin da uwar jam’iyyar ta zantar.

Jam’iyyar ta zargi Madaki a lokuta daban-daban yana hada kai da shugaban karamar hukumar Abuja ta tsakiyar domin bayar da bayanan karya a kan zaban fidda gwani da jam’iyyar ta samu nasarar kammalawa domin raba kan ‘ya’yan jam’iyyar da jefa kiyayya a tsakaninsu.

“Ka kasa gabatar da cikakken bayani da zai hada kan mambobin jam’iyyar. Dukkan bayananka na wargaza hadin kan jam’iyyar ne wanda suka janyo kiyayya a cikin gundumar ba tare da la’akari da matsayin ka a cikin jam’iyyar ba.

“Kana daukan kanka a matsayin mai zantarwa kai kadai, inda kake daukan hukunci da zantarwa ba tare da bin ka’idojin jam’iyyar ba da kuma kin amincewa da sauran ‘yan takarar da su sami damar da masu zantarwa a gundumar suka shardanta kafin zaban fidda gwani.

“A kwanakin nan, kana ta amfani da kayayyakin jam’iyyar a matsayin naka ba tare da sanin sauran shugabannin jam’iyyar ba.

“Sakamakon abubuwan da aka bayyana a baya, mu mambobin zantarwa na jam’iyyar APC a gundumar Jiwa, mun dakatar da Alhaji Bala Madaki daga jam’iyyar APC bisa rashin da’a da cin amanar jam’iyya da saba wa dokokin jam’iyyar APC,” in ji jam’iyyar.

Exit mobile version