Daga Abdullahi Sheme,
A ranar Litinin din da ta gabata 15 ga Fabrairu, 2021, ne tunda misalin karfe 10 na safiyar ranar dubban magoya bayan Sanata Ahmed Babba Kaita Sanata mai wakiltar shiyyar Daura ‘ya’yan jam iyar APC daga kananan hukumomi 34 na jihar Katsina suka yi fitar farin dango, domin rufa wa Sanata Ahmed Babba Kaita, domin sabunta katin rijistar jam’iyarsa ta APC a akwatin da yake jefa kuri’arsa a makarantar firamare ta Sada da ke cikin garin Kankiya a mazabar Galadima ‘A da ke cikin karamar hukumar Kankiya ta jihar Katsina.
Sanata Kaita ya sami gagarumin tarba daga dukkan magoya bayansa na’ya’yan jam’iyar APC da ke jihar Katsina inda a ka rufe hanyar da ta taso daga Katsina ta biyo ta Kankiya ta wuce Kano, saboda yawan magoya baya da motoci da tawagar ta chunkushe hanyar na sama da awoyi 4 kafin a isa filin makarantar sada inda Sanatan zai sabunta katin rijistar tashi.
A jawabin da ya yi wa magoya bayansa ya ce, a rayuwarsa ba zai taba mantawa da wannan muhimmiyar rana ba ganin yadda dubban magoya baya suka rakoshi daga kananan hukumomi 34 dake nan jihar wannan ba karamin alheri ba ne kuma ya ce, ya godewa Allah da dukkan magoya bayansa wadanda suka zo daga nesa dama na kusa Sanatan wanda yake jawabin kuma yana zubar da hawayensa saboda ganin yadda a ka nuna mashi kauna da karamci da son jam’iyarsu ta APC.
Sanata Ahmed Babba Kaita yana nan a jam’iyar APC daram daram kuma zai ci gaba da bada gudunmawarsa da taimakon al’umma kamar yadda saba daga nan ya yi kira da kakkausar murya ga dukkan Gwamnonin kasar nan da su kara hada kawunansu waje guda don ciyar da kasar nan gaba kuma su kawo karshen yadda a ke yi wa ‘ya ‘yan bora da na mowa musamman mutanen mu wadanda suke zaune a kudancin kasar nan yadda a ke wulakanta mana su abin ba zai yiwu ba domin Nijeriya kasa daya ce.
Kuma kowa yana iya zama inda ya keso ya ce yawan kashe mutanen da a keyi da satar jama’a da a keyi domin neman kudin fansa da yadda ‘yan ta’adda suke ta addanci wadansu jihohin kasar nan abin ya yi yawa dole su kara dagewa suga Gwamnatin tarayya da Gwamnatocin jihohin kasar nan sun kawo karshen wannan matsalar tsaron da ya addabi al’umma.
Alhaji Babba Kaita ya ce yana kara kira da a bar kowanne dan jam iyar APC ya sabunta katin rijistar shi dama wanda yake da sha’awar shigowa jam ‘iyar kada a boye ko a hana wani katin sabunta rijistar.
Daga karshe ya ce tarihi ne zai maimaita kanshi ya ce a Nan garin kankiya an taba hanashi rijista Kuma Allah cikin ikonsa ya kuma lashe zabensa. Sanatan ya kuma ce, kasan komai daga Allah ne shi keba mutum mulki yakuma karbe daga hannun wanda yake so ya godema Allah da dukkan magoya bayanshi musamman wadanda suka zo daga kananan hukumomin nesa daga yankin Karaduwa watau shiyyar funtuwa da Katsina da na gida shiyyar Daura.
Kuma yayi addu’ar Allah ya maida kowa gidan shi lafiya amin wakilinmu yagano kuma ya zanta da wasu daga cikin mutanen da suka rufama Sanatan baya musamman wadanda suka fito daga mazabar shiyyar Funtuwa dana Katsina kamar wadanda suka fito daga kananan hukumomi 11 na shiyyar funtuwa da na shiyyar Katsina bai rasa nasaba da yadda ya taimaki yankunan nasu sun nuna godiyarsu a kan yadda ya samar wa yaransu aiki da gina masu makaratun boko da na Islamiyyu da ya yi masu da yadda Sanatan ya dauki yaransu masu yawa aikin a ma’ aikatun Gwamnatin tarayya wadanda ba ma a mazabar shi suke ba, dukkan kananan hukumomi 34 dake fadin jahar Katsina.
Saboda wadannan manyan aiyukan da taimakon al’umma da yadda ciyar da matasan jahar gaba yasa jama’a sukazo don kashin kansu domin su rufama Sanatan baya Wajen Sabunta Katin Rijistar shi a jam iyar APC Kuma masana tarihin siyasar jahar sunce ba a taba samun Sanata kamar Ahmed Babba Kaita ba kuma suna yi mashi fatan Allah ya ba shi wata babbar kujerar da tafi wadda yake Kai a halin yanzu mawaka da makada da ‘yan bankaura da sauran masu wasan kwaikwayo suka halarci taron.