Abba Ibrahim Wada" />

Arsenal Da Liverpool Suna Rige-Rigen Siyan Dembale

Wasu rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa kungiyoyin Arsenal da Liverpool ne suke rige rigen siyan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Lyon ta kasar Faransa, Moussa Dembele, dan asalin kasar ta Faransa.

Dembele mai shekara 22 a duniya wanda ya koma Lyon daga kungiyar kwallon kafa ta Celtic dake kasar Scotland ya zura kwallaye 20 cikin wasanni 45 daya bugawa Lyon kuma yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan kasar Faransa.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ma tana zawarcin dan wasan wanda ya zura kwallaye 51 cikin wasanni 94 daya bugawa kungiyar Celtic kafin yabar kungiyar inda ake tunanin shine zai maye  gurbin Rumelu Lukaku wanda yake son komawa Inter Milan da buga wasa.

Sai dai Manchester United tana fuskantar kalubale daga wajen Liverpool da Arsenal wadanda suma suka nuna aniyarsu ta siyan matashin dan wasan wanda a a yanzu yake wakiltar tawagar matasa ta ‘yan kasa da shekara 23 ta kasar Faransa.

Duka kungiyoyin Arsenal da Manchester United da Liverpool din suna zawarcin dan wasan gaba bayan da dan wasa Daniel Sturridge yabar Liverpool sannan kuma ana ganin shima Lukaku bazai cigaba da zaman United ba.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Lyon batason rabuwar  da dan wasan kuma idan har zata siyar dashi bazata siyar dashi da araha ba kamar yadda shugaban kungiyar Jean Macahel-Aulas ya bayyana a kwanakin baya.

Exit mobile version