Daga Khalid Idris Doya,
Wani yaro mai suna Amos da wasu mutum hudu ne suka rasa rayukansu yayin artabu tsakanin kungiyoyin asiri guda biyu a kauyen Lobia II da ke yankin kudancin karamar hukumar Ijaw a jihar Bayelsa.
A cewar ganau kan lamarin, kungiyoyin asirin sun fito ne daga unguwannin Ukubie da Azuzuama wanda kuma fada ta shiga tsakaninsu ne dai a ranar Lahadi a wajen bikin tunawa da wani marigayi Chief Genesis a Lobia II sai dai har zuwa yanzu ba a gano musabbabin abun da ya jawo artabun ba.
Da aka tuntubi Kakakin ‘yan sandan jihar SP Asinim Butswat ya shaida cewar kawo yanzu ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, inda ya ce yana kan kokarin tuntubar DPO din yankin da lamarin ya faru domin jiyowa daga gareshi, ya ba tabbacin nayar da cikakken bayanin lamarin da ya faru idan ya kammala tattare da bayanai.