DAGA SADIK TUKUR GWARZO
Cigaba daga makon jiya
Ai a zahirin yakin da Turawa su ka yi a zamanin mulkin mallaka da ’yan kasa a ka yi, domin mafi yawan dakarunsu ‘yan kasa ne bakaken fata, tunda Turawa ba yawa gare su ba a rundunonin, hasali ma wannan yanki namu kamar makabarta ya zamewa Turawa, saboda yawaitar cututtuka da ke yi mu su lahani.
Idan kuma ba haka ba, to za mu iya cewa ba ya daga cikin manufar Turawa a zuwansu wannan yanki su inganta addinin Islama tunda a nasu ganin rubutun ajami na Musulunci ne. Dalili kenan da ba za su yarda su yi aiki da rubutun ajami ba ballantana har su inganta shi.
Don haka a ka ce babbar sadarwar da sojojin Luggard su ka fi fahimta daga gare shi ita ce rashin son sa ga Musulunci. A zahiri, ban jin an taba ruwaito wata kalma ta batanci da Luggard ya yiwa Islama, amma a badini ayyukansa na son ganin ya habaka addininsa ne tare da cika umarnin kasarsa.
Shi ya sa kuma sojojinsa su ka fi kaunar ko me za a rubuta mu su, a rubuta mu su shi da yaren Hausa, yaren da su ka fi sha’awar yarawa sama da nasu, amma kuma cikin haruffan sabuwar wayewa da Turawa kuma Kiristocin mulkin mallaka su ka kawo, watau Romanci.
Bayan an ci Kano da Sokoto da yaki, sai Gwamna Lugga ya sa a ka yi ma sa hasashen daliban da ke makarantun allo a wannan yanki, inda kintace ya nuna cewa akwai misalin makarantun allo da ake karantar da addinin Musulunci cikin rubutun Arabi da Ajami kusan 25,000, sannan daliban da ke cikin makarantun sun tasamma 250,000.
Wannan ta sa Lugga fahimtar cewa akwai aiki ja agabansa, amma dai an ce da taimakonsa a ka kafa makarantar mishan a Bidda a cikin shekara ta 1904, inda aka fara koyawa wasu mutane ciki harda tsirarun musulmai rubutun Hausar Boko, gami da harshen Turanci. An ce a na koyar da daliban ne cikin harsunan mu na gida, watau Hausa da Nufanci.
Gwamna Lugga ya sanar da Ingila yunkurin daya fara na juya rubutun ajami izuwa haruffan Rumawa (Boko) kamar yadda aka samu a kundin takardun dayasha turawa izuwa ingila (Annual Report, Northern Nigeria no. 476, 1903, 332-3).
Daga sanda a ka fara samun gagarumar nasara a fannin rubutun Boko a kasar Hausa kuwa shi ne wajejen shekara ta 1908, sa’ar da Lugga ya tura Dr. Hans Bischer wanda a ka fi sani da ‘Dan Hausa’ izuwa kasashen Sudan, Misira (Egypt) da Gwalkwas (Ghana) domin yin nazari akan yadda kasashen ke bayar da ilimi ga mutanensu wadanda akasari musulmai ne, saboda kasancewar Hausawa musulmai sunki tura ‘ya’yansu a harkar Boko.
Bayan Dr. Bischer ya dawo gida ne akace ya bude makarantar elementary da ake kira Makarantar Dan Hausa a Nassarawan jihar kano, wadda akace da dalibai 30 ta soma waɗanda sukazo daga maban-bantan yankuna da kuma kabila, sai a hankali daliban suka rinka yawaita.
Amma dai daga wannan lokacin ne aka samu cewar an fara fassara littattafai na ilimi wadanda aka rubuta su a wasu yarukan duniya izuwa Hausa, aka yi rubutun nasu kuma da rubutun Boko, a sannan ne kuma gwamnati ta mayar da Hausa a yankin arewa a matsayin yaren sadarwa (abinda kusan ya jazawa kowacce kabila dake yankin fara koyon harshen Hausa kenan), sannan kuma a hankali har hukumar fassara ta jihar arewa da akafi sani da ‘Norla’ tazo wadda itama ta bada gagarumar gudunmuwa wajen fassara manyan littattafan ilimi masu amfani izuwa harshen Hausa.
Daga littattafan farko da aka soma fassarawa izuwa harshen Hausa da rubutun Boko a wanban lokaci akwai misalin :- Koyon Lissafi, Dare Dubu da daya, Tarihin Garuruwan Borno, da wasu littattafan da dama.
Daga wannan nake ganin ta haka rubutun Hausar Boko yaci galaba akan ruɓutun ajami da gagarumar nasara, domin rubuce-rubucen da aka ka yi na ilimi kusan sun dararwa wadanda aka rubuta da Hausar ajami zuryan. Don haka sai bukatuwar ilimi ga jama’a ya tursasasu kpyon harufgan Boko don ganewa sama da koypn haruffan Hausar ajami. A yanzu munkai munzalin da dalibi zai kammala digirin digirgir ba tare daya karanta wani littafi a ajami ba.
BUNKASAR HARSHEN HAUSA
A bisa fahimta irin tamu, yaren Hausa gamayya ce ta haifar da shi. Littafin Babil mai tsarki ya fadi cewar shekaru da dama da suka gabata (misalin shekaru dubu takwas da suka gabata), mutanen duniya da harshe daya kurum suke amfani, sai daga baya yaruka suka rinka samuwa ta yadda zuwa yanzu akwai kimanin yaruka dubu bakwai a fadin duniyar nan. Ina tsammanin Littafin Alkur’ani maigirma bai yi magana irin wannan ba, amma duk da haka maganar data fito daga Babil na iya tabbatuwa a kimiyance tunda dai munsan cewa Allah Ubangiji ne ya saukar da littattafan duka guda biyu.
Samuwar harshen Hausa na iya zamowa daga hadakar kalmomi na wadansu yaruka mabanbanta. Ma’ana, tana iya kasancewa karo-karon kalmomi daga yaruka daban-daban ne ya hadu ya samar da yaren Hausa kachokan dinsa, hakan kuwa na iya faruwa ne idan muka kalli Hausawan su kansu zamuga cewa kabilu ne da dama suka cakudu suka rikide tare da zamowa Hausawa lokaci mai tsawo daya shude.
Misali, bari mu dauki manyan garuruwan Hausa mu dan yi karamin nazari akansu:-
A tarihin kafuwar kano, ance wani mai suna Dala ne ya fara zama akan wani dutse wanda daga bisani aka sanya masa suna dala. A hasashe, hakan ta faru tun a wajajen karni na bakwai. Littafin tarihin kano da ake kira ‘Kano Chronicle’ (Tarih baladil Laziy Musamma Kano) ya ruwaito kwatankwacin haka, har kuma ya rubuta a shafin farko “La na’alamu k’abilatihi’.
Za mu cigaba a makon gobe in sha Allahu