Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Asibitocin Wuhan Sun Kawo Karshen Jinyar Masu Dauke Da Cutar COVID-19

Published

on

Masu hikimar magana na cewa hannu daya baya daukar jinka kuma himma baki ga raggo, tun bayan da aka fuskanci wahalhalu a kusan watanni uku da suka gabata a birnin Wuhan dake lardin Hubei inda aka samu barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, gwamnatin kasar Sin da al’ummar Sinawa sun zama tamkar tsintsiya madaurinki daya wajen yin hadin gwiwa da juna domin tinkarar aikin kandagarki da kuma dakile annobar da ta barke. Idan zamu iya tunawa, tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar ta Sin, gwamatin kasar ta himmatu wajen daukar kwararan matakan da suka dace cikin gaggawa, misali killace birnin Wuhan ba shiga ba fita inda aka samu barkewar cutar gami da tantance daukacin mutanen da suka yi cudanya da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar, hakan ya sa ta yi nasarar hana yaduwar annobar a tsakanin jama’a da ma sauran sassan kasar har ma da kasa da kasa. Wadannan matakai da kasar Sin ta dauka sun janyo mata yabo daga shugabannin duniya da na shiyyoyi gami da kungiyoyin kasa da kasa musamman hukumar lafiya ta duniya WHO da MDD da dai sauransu.

Bayan shafe wa’adin watanni ana fadi tashin ganin bayan annobar a birnin Wuhan da sauran larduna da yankunan kasar Sin, hakika za’a iya cewa haka ta cimma ruwa domin kuwa an samu manyan nasarorin da ake bukata, misali a ranar 8 ga watan Afrilun aka dage haramcin tafiye-tafiye a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar bayan shafe kusan makonni 11 yana rufe da nufin takaita yaduwar cutar COVID-19, motoci da jiragen kasa da na sama sun shirya barin birnin. Yayin da kamfanoni su ma suka koma bakin aikinsu. Hukumomin kula da sufurin jiragen kasa sun gargadi masu tafiye tafiye da su bayar da hadin kai wajen duba lafiyarsu lokacin shiga tasoshi, da sauran wuraren hada hadar yau da kullum domin rage hadarin kamuwa da cutar.

A ranar 23 ga watan Janairu ne aka ayyana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a Wuhan, ciki har da motocin haya na birnin da jirgen sama da na kasa, a wani yunkuri na dakile yaduwar annobar COVID-19. Wani labari mai faranta shi ne, bayan shafe wannan tsawon lokaci ana aikin kandagarki da yaki da annobar, ya zuwa ranar Lahadi da ta gabata, asibitocin dake birnin Wuhan sun kammala aikin jiyyar dukkan mutanen da aka kwantar da su a asibitoci bayan da aka tattabar suna dauke da cutar COVID-19. Mi Feng, shine kakakin ma’aikatar lafiyar kasar Sin ya fadawa taron manema labarai a Beijing cewa, an samu wannan gagarumar nasara ne sakamakon jajurcewa da aiki tukuru na jami’an lafiyar Wuhan da sauran jami’an lafiyar da aka tura daga sauran sassan kasar Sin zuwa lardin Hubei da birnin Wuhan inda cutar ta barke.

Sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi ta nuna cewa, a halin yanzu an yi nasarar dakile yaduwar annobar COVID-19 a cikin gidan kasar Sin.

An danganta nasarorin da aka samu bisa jerin cikakkun matakai da aka dauka da dokokin da gwamnatoci suka shimfida bisa shawarwarin da kwararrun masana lafiya na kasar suka bayar da nufin dakile annobar. Daga ranar 23 ga watan Janairu an killace birnin Wuhan wanda ya shafe tsawon kwanaki 76 a kulle. Shugabannin kasar Sin sun sha nanata aniyarsu na mayar da rayuwar jama’a da kuma lafiyar al’ummar kasar bisa matsayin koli, kana hukumomin sun bada umarnin kula da lafiyar dukkan majinyatan da suka kamu da cutar don ceto rayuwarsu. A birnin Wuhan, an kafa asibitocin wucin gadi masu yawa domin jinyar mutanen da suka kamu da annobar COVID-19, kimanin asibitocin wucin gadi 16 aka bude, wanda ke kunshe da gadaje kimanin 60,000 don kula da majinyatan. Sama da jami’an lafiya 42,000 aka tura zuwa lardin Hubei daga sassa daban daban na kasar Sin, da kuma tura kayan ayyukan kiwon lafiya da suka hada da na’urar taimakawa numfashi, da rigunan bada kariya ga jami’an lafiya, da takunkumin rufe fuska, da sauran kayayyakin bukatun yau da kullum.

Hakika, kasar Sin ta taka rawar gani wajen kawar da annobar COVID-19 a kasar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: