Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya ce jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar ba sa tsoron duk wani bincike da ake shirin yi wa dan takarar.
Da yake magana kan zargin karkatar da kudade, Melaye ya ce Atiku ne dan Nijeriyar da a aka fi bincika kuma ba a taba samunsa da laifi ba.
- Sin Za Ta Kara Inganta Hadin Gwiwar Dake Tsakaninta Da Kasashen Afirka
- NNPP Ta Yi Mummunar Bari A Arewa Maso Gabas
Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ne, ya bayyana hakan a cikin shirin siyasar gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Melaye ya ce Atiku a koda yaushe yana mika kansa domin bincike shi ba kamar yadda wasu ke dauka ba.
“Atiku Abubakar mai bin dimokradiyya ne; dan Nijeriya ne. Ya kasance a shirye ko yaushe don yin bincike a bincike shi.
An bincike shi a baya kuma ya fito ba tare da wani laifi ba.
“Don haka ba ma tsoron bincike, domin shi ne dan Nijeriya da aka fi bincika kuma idan ka sake bincikarsa zai fito ba tare da wani laifi ba,” in ji shi.
Melaye ya jaddada cewa ya kamata a binciki takwaran Atiku na jam’iyyar APC, Bola Tinubu tare da gurfanar da shi gaban kotu.
“Shi ne wanda ya fi cancanta a gurfanar a gaban kotu, saboda akwai zarge-zarge masu yawa a kansa ba ya ga rashin sanin hakikanin asalin inda ya samo dukiyarsa,” in ji shi.
Tun da farko dai an saki wani sautin murya a satin da ya gabata, inda aka ji wata murya mai kama da Atiku da wani jami’in gwamnati suna tattauna yadda aka yi fadi da wasu makudan kudade.