Dandalin Al’adu Na Beijing Zai Mayar Da Hankali Ga Batun Gadon Al’adu Da Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai
An kaddamar da dandalin al’adu na birnin Beijing na shekarar nan ta 2026 a jiya Talata, dandalin da ya hallara sama da baki 600 daga kasashe da yankunan duniya 44, don tattaunawa kan kare al’adun da aka gada daga kaka da kakanni, da koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai. Li Shulei, shugaban sashen yayyata ayyukan JKS na kwamitin kolin jam’iyyar, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. Mahalarta dandalin daga bangaren Sin da na kasashen ketare sun bayyana shawarar inganta wayewar kan duniya da Sin ta gabatar, tare da sauran matakai na ingiza hadin gwiwar kasa da kasa a fannin al’adun gado, da samar da al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, a matsayin muhimman manufofi na bunkasa al’adun da aka gada daga kaka da kakanni a Sin da ma sauran sassan duniya. Sun kuma bayyana gadon al’adu a matsayin wata kadara ta daukacin bil’adama, kuma kare ta, da gadar da ita, da kyakkyawan amfani da ita a matsayin muhimman matakai na ci gaba da wanzar da wayewar kai na bil’adama da wanzar da ci gaban duniya. Bugu da kari, mahalarta dandalin sun yi kira da a karfafa kwazo wajen kare gadon al’adun dan’adam, da nacewa ka’idojin kariya da farko, da amfani da su yadda ya kamata, da takaita tsoma hannu cikin tsarin baiwa al’adun kariya, da kare al’adun gado tamkar yadda muke kare rayukanmu. (Saminu Alhassan)



















