Liu Guozhong, mamba a ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma mataimakin firaministan kasar, ya kai rangadin aiki a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin daga ranar 21 zuwa 23 ga wata, inda kuma ya halarci shagulgulan bikin girbi na manoma na Sin na shekarar 2026.
Liu ya jaddada cewa, ya kamata a tada himma da karfafa gwiwar manoma, da kuma hada karfin sassa daban-daban na al’umma, da hanzarta zamanantar da sha’anin noma da raya karkara, kana da gina kauyuka masu kyau da suka dace da jin dadin zama da aiki bisa yanayin da suke ciki, sannan a inganta farfado da karkara a dukkan fannoni. (Bilkisu Xin)
ADVERTISEMENT














