ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

by CGTN Hausa
5 hours ago
Sin

Yau ranar 23 ga watan Satumba ita ce ranar bikin girbi na manoman kasar Sin karo na 9. A daidai wannan lokaci mai farin ciki, bari mu duba wasu alkaluma masu alaka da ci gaban ayyukan noma na Sin. A shekarar 2025, yawan amfanin gona na Sin ya ci gaba da kasancewa da adadin tan miliyan 700, kuma yawan gonakin noma masu inganci da aka kafa ya kai sama da hekta miliyan 66.67. Yawan matsakaicin kudin shiga na kowane mazaunin karkara ya kai yuan 24456, wanda ya karu da kashi 6% idan an kwatanta da shekarar da ta gabaci hakan, har yawan karuwarsa ya fi na mazauna birane da kashi 1.8%. Har ila yau, kason ayyukan gona da aka gudanar da injuna a fadin kasar ya wuce kashi 76%, kuma gudummawar da fasahohin zamani suka bayar ga ci gaban aikin noma ya wuce kashi 64%. 

Lallai ci gaban da Sin take samu a fannin aikin noma na da alaka matuka da kwaskwarimar da take yi a wannan fanni, wato yadda ta karkata daga “dogaro da yanayi” zuwa “raya fasahohin zamani”. Kuma dabarun da Sin take samu daga ayyukan gona suna kuma amfanar da nahiyar Afirka. 

A kauyen Midekin na Chadi, gonakin gwaji da tawagar kwararrun aikin gona ta Sin suka kafa a wurin, suna iya samar da shinkafa sama da tan 10.03 a kan kowace hekta, wanda ya kusan ninka matsakaicin yawan shinkafar da a kan samu a wurin har sau 3. Tawagar kuma ta gina karamar masana’antar sarrafa shinkafa, inda ta hakan ake iya “girbe shinkafa da safe, tare da sarrafa su da tsakar rana kuma a sayar da su da yamma”. 

ADVERTISEMENT

Sai kuma a lardin Mashonaland ta Yamma na Zimbabwe, tawagar kwararrun Sin ta gina “gidan renon kaji”, inda ake amfani da injin kyankyashe kwan kaji da Sin ta kera, kuma yawan kaji da inji ke iya kyankyasa a kowane wata ya haura sama da 2000. Hakan ya sa mazaunin wani kauye Nomusa Ncube ke iya samun kudin shiga kusan dala 320 a kowane wata, wanda da hakan muke ganin cewa, fasahohin kasar Sin ta kara wa manoman Afirka karfin aljihunsu. 

Har wa yau, Samson Mofolo, dalibin da ya yi karatun digiri na 3 da jami’ar aikin gona ta kasar Sin ta horar karkashin shirin hadin gwiwar Sin da Afirka a bangaren aikin noma, yanzu haka yana aiki a cibiyar yada fasahar noma ta gundumar Lisasadzi ta Malawi, yana kokarin koyar da fasahohi masu alaka da taki, da shuka iri. Yanzu amfanin gona da ake shukawa a gonaki na zama kudin shiga ga manoma. 

LABARAI MASU NASABA

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

Duk matakan da Sin take dauka a Afirka na bayyana cewa, ba kawai ba da kudi da kaya kasar Sin take yi ba, tana kuma kai fasahohin noma da dabarunta da tsarin harkokin masana’antu zuwa Afirka, domin taimaka wa manoman Afirka su dogara da karfin kansu. 

Ban da wannan kuma, a ranar 1 ga watan Mayu na bana, Sin ta fara aiwatar da manufar soke gaba dayan harajin kwastam kan kasashen Afirka 53 da ke da huldar diflomasiyya da ita, wanda hakan ya sa kayayyakin noma masu inganci na Afirka suke iya shiga kasuwar Sin ba tare da biyan haraji ba. Kayayyakin noma na Afirka ba wai kawai yawansu ya karu ba, har ma hanyar sayar da su ma ta habaka. 

Samun girbi mai armashi ba nasara ga kasar Sin ba kadai, haka kuma nasara ce ta hadin gwiwar Sin da Afirka. Yayin da manoman Sin ke murnar bikin girbi, a sa’i daya kuma manoman Afirka ma suna cin gajiya. 

Bikin girbi na manoma ba wai kawai murna da yin girbi mai armashi a wata shekara ba ne, har ila yau ya kasance amsa ga tambayar “yaya za a samu isasshen abinci”. Sin ta kwashe shekaru da dama tana warware wannan matsala, kuma yanzu tana kokarin taimaka wa Afirka wajen warware wannan matsala bisa fasaha da iliminta. 

Gonakin shinkafa na Chadi, gidan kaji na Zimbabwe, aikin hadin gwiwar Sin da Afirka na fasahar noma na Malawi da sauransu, dukkansu sun bayyana yadda dabarun Sin ke amfanar da al’ummar Afirka, kuma girbin manoman Afirka zai zama wata kyakkyawar shaida ga zumunci da hadin gwiwarsu.(Marubuciya: MINA)  

Sin
CGTN Hausa
+ postsBio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Aika Da Wasikar Taya Murna Ga Gasar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Karo Na 48

MASU ALAKA

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana
Daga Birnin Sin

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

September 23, 2026
Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

September 23, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

LABARAI MASU NASABA

Sultan

Kada Ku Ɗauki Nauyin Aikin Hajji Da Kuɗaɗen Da Aka Sace — Sultan Ga ’Yan Siyasa

September 23, 2026
Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

September 23, 2026
Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

September 23, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

September 23, 2026
Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

September 23, 2026
An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

September 23, 2026
TMG Ta Buƙaci Atiku Da Obi Su Haɗa Kai Don Kayar Da Tinubu A 2027

TMG Ta Buƙaci Atiku Da Obi Su Haɗa Kai Don Kayar Da Tinubu A 2027

September 23, 2026
Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

September 23, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.