ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

by Khalid Idris Doya
54 minutes ago
Fansho

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnatin jihar Bauchi ta fara rage tulin basukan giratuti da tsofaffin ma’aikata ke binta ta hanyar fara biyan Naira biliyan goma domin rabawa wa tsofaffin ma’aikatan gwamnati 1,700 da suka gama aikinsu tsawon shekaru a matakin jiha da ƙananan hukumomi.

Da ya ke magana a wajen ƙaddamar da aikin tantancewa da biyan kuɗaɗen a karo na farko, Gwamna Bala Mohammed ya ce biyan kuɗaɗen ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin na shawo kan tarin bashin giratuti da tsofaffin ma’aikatan ke bin gwamnatin jihar.

ADVERTISEMENT

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Gwamnan, Muhammad Auwal Jatau, ya ce wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan gwamnati sun shafe sama da shekaru 10 suna jiran samun haƙƙoƙinsu, bayan sun kwashe shekaru suna yi wa jihar hidima.

Ya ce kashin farko na biyan kuɗaɗen zai shafi waɗanda suka yi aiki a ƙananan hukumomi tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013, yayin da na ma’aikatan gwamnatin jihar zai fara daga shekarar 2013. Ya ƙara da cewa za a ci gaba da biyan sauran shekarun da kashi-kashi bisa tsari.

LABARAI MASU NASABA

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

Ya ce, “Lokacin da muka karɓi ragamar mulkin Jihar Bauchi, mun gaji tarin bashin giratuti da ya samo asali tun daga shekarar 2012. Abu ne da kowa ya sani cewa tarin bashin giratuti ya kasance ɗaya daga cikin manyan matsalolin kuɗi da suka addabi gwamnatocin da suka gabata a jihar.”

Gwamnan ya ce, “Yan fanshonmu ku ne iyayenmu, malamai da masu ba mu shawarwari. Kun shafe shekaru 35 na ƙuruciyarku, ƙarfinku da basirarku wajen gina ababen more rayuwa, makarantu, tsarin kiwon lafiya da kuma tsarin gudanar da harkokin gwamnatin Jihar Bauchi,” don haka ne ya ce su ba abun wulaƙantawa ba ne dole a girmamasu.

Gwamnan ya nuna nadama kan yadda wasu daga cikin ma’aikatan da suka yi ritaya suka rasu yayin da suke jiran haƙƙoƙinsu ba tare da sun samu damar amsa ba.

Ya ce, “Rashin tsarin da ya dace ne kuma rashin adalci ne idan ma’aikaci ya kammala aikin da ya yi wa ƙasa ko jiha hidima yadda ya kamata, sannan ya shafe shekaru yana jiran samun haƙƙoƙin da ya tara kuma ya kasa samu.”

Ya bayyana cewa gwamnatin ta kafa hukumar kula da fansho ta Jihar Bauchi domin inganta yadda ake tafiyar da harƙoƙin fansho da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukan.

A cewarsa, an kafa wani babban kwamiti ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabiu Baba, domin kula da tantance bayanan tsofaffin ma’aikata, tabbatar da sahihancin bayanai da kuma rabon kuɗaɗen.

Mohammed ya ce, “Kwamitin ya yi aiki tuƙuru wajen tsara hanyoyin da za su tabbatar da cewa kowane kobo ya isa hannun wanda yake da haƙƙin karɓarsa kai tsaye, ba tare da tsaiko na hukumomi ba.”

Gwamnan ya shaida wa sauran tsofaffin ma’aikatan da ba su cikin masu samun kuɗaɗen a karon farko da cewa su kwantar da hankalinsu ana ƙoƙarin yadda su ma za a biya su. Yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan sauran kuɗaɗen bisa tsari, bayan tantance bayanai da kuma la’akari da kuɗaɗen da suke akwai a lalitar jihar.

“Mun fara daga nan, amma ba a nan za mu tsaya ba,” in ji shi.

Gwamnan ya umarci jami’an da ke gudanar da aikin da su tabbatar an yi wa waɗanda za su amfana da shirin mu’amala cikin mutunci da adalci.

Ya ce, “Kada a samu wani tsaiko na ofis, son rai ko karɓar kuɗin haram. Kada a sanya tsofaffin ma’aikatan cikin halin wulaƙanci yayin tantancewa. A tabbatar an bai wa tsofaffi masu naƙasa ko waɗanda ke cikin rauni fifiko da kulawa cikin sauƙi.”

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) reshen Jihar Bauchi, Comrade Dauda Shehu, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa fifita jin daɗin ma’aikata.

Shehu, wanda Ibrahim Maikudi ya wakilta, ya ce Bauchi na daga cikin jihohin farko a ƙasar da suka fara aiwatar da mafi karancin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati.

Ya kuma ce Bauchi ita ce jiha ta farko a Arewacin Nijeriya da ta fara aiwatar da mafi ƙarancin fansho na naira 32,000 ga ’yan fansho.

Shi ma da yake magana a madadin shugabannin ƙananan hukumomi, Shugaban Karamar Hukumar Ningi, Alhaji Yahuza Adamu, ya ce biyan kuɗaɗen giratuti abu ne da zai iya farfaɗo da tattalin arzikin jihar.

Yahuza ya ce biyan kuɗaɗen ya cika wani dogon buri da ’yan fansho suka daɗe suna jira, yana mai cewa gwamnatocin baya sun yi alƙawarin magance matsalar tarin bashin giratuti amma sun kasa.

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara Biyan Naira Biliyan 10 Ga ‘Yan Fansho 1,700Daga Khalid Idris Doya Gwamnatin jihar Bauchi ta fara rage tulin basukan giratuti da tsofaffin ma’aikata ke binta ta hanyar fara biyan Naira biliyan goma domin rabawa wa tsofaffin ma’aikatan gwamnati 1,700 da suka gama aikinsu tsawon shekaru a matakin jiha da ƙananan hukumomi.Da ya ke magana a wajen ƙaddamar da aikin tantancewa da biyan kuɗaɗen a karo na farko, Gwamna Bala Mohammed ya ce biyan kuɗaɗen ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin na shawo kan tarin bashin giratuti da tsofaffin ma’aikatan ke bin gwamnatin jihar.Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Gwamnan, Muhammad Auwal Jatau, ya ce wasu daga cikin tsofaffin ma’aikatan gwamnati sun shafe sama da shekaru 10 suna jiran samun haƙƙoƙinsu, bayan sun kwashe shekaru suna yi wa jihar hidima.Ya ce kashin farko na biyan kuɗaɗen zai shafi waɗanda suka yi aiki a ƙananan hukumomi tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013, yayin da na ma’aikatan gwamnatin jihar zai fara daga shekarar 2013. Ya ƙara da cewa za a ci gaba da biyan sauran shekarun da kashi-kashi bisa tsari.Ya ce, “Lokacin da muka karɓi ragamar mulkin Jihar Bauchi, mun gaji tarin bashin giratuti da ya samo asali tun daga shekarar 2012. Abu ne da kowa ya sani cewa tarin bashin giratuti ya kasance ɗaya daga cikin manyan matsalolin kuɗi da suka addabi gwamnatocin da suka gabata a jihar.”Gwamnan ya ce, “Yan fanshonmu ku ne iyayenmu, malamai da masu ba mu shawarwari. Kun shafe shekaru 35 na ƙuruciyarku, ƙarfinku da basirarku wajen gina ababen more rayuwa, makarantu, tsarin kiwon lafiya da kuma tsarin gudanar da harkokin gwamnatin Jihar Bauchi,” don haka ne ya ce su ba abun wulaƙantawa ba ne dole a girmamasu.Gwamnan ya nuna nadama kan yadda wasu daga cikin ma’aikatan da suka yi ritaya suka rasu yayin da suke jiran haƙƙoƙinsu ba tare da sun samu damar amsa ba.Ya ce, “Rashin tsarin da ya dace ne kuma rashin adalci ne idan ma’aikaci ya kammala aikin da ya yi wa ƙasa ko jiha hidima yadda ya kamata, sannan ya shafe shekaru yana jiran samun haƙƙoƙin da ya tara kuma ya kasa samu.”Ya bayyana cewa gwamnatin ta kafa hukumar kula da fansho ta Jihar Bauchi domin inganta yadda ake tafiyar da harƙoƙin fansho da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukan.A cewarsa, an kafa wani babban kwamiti ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Sabiu Baba, domin kula da tantance bayanan tsofaffin ma’aikata, tabbatar da sahihancin bayanai da kuma rabon kuɗaɗen.Mohammed ya ce, “Kwamitin ya yi aiki tuƙuru wajen tsara hanyoyin da za su tabbatar da cewa kowane kobo ya isa hannun wanda yake da haƙƙin karɓarsa kai tsaye, ba tare da tsaiko na hukumomi ba.”Gwamnan ya shaida wa sauran tsofaffin ma’aikatan da ba su cikin masu samun kuɗaɗen a karon farko da cewa su kwantar da hankalinsu ana ƙoƙarin yadda su ma za a biya su. Yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan sauran kuɗaɗen bisa tsari, bayan tantance bayanai da kuma la’akari da kuɗaɗen da suke akwai a lalitar jihar. “Mun fara daga nan, amma ba a nan za mu tsaya ba,” in ji shi.Gwamnan ya umarci jami’an da ke gudanar da aikin da su tabbatar an yi wa waɗanda za su amfana da shirin mu’amala cikin mutunci da adalci.Ya ce, “Kada a samu wani tsaiko na ofis, son rai ko karɓar kuɗin haram. Kada a sanya tsofaffin ma’aikatan cikin halin wulaƙanci yayin tantancewa. A tabbatar an bai wa tsofaffi masu naƙasa ko waɗanda ke cikin rauni fifiko da kulawa cikin sauƙi.”Da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) reshen Jihar Bauchi, Comrade Dauda Shehu, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa fifita jin daɗin ma’aikata.Shehu, wanda Ibrahim Maikudi ya wakilta, ya ce Bauchi na daga cikin jihohin farko a ƙasar da suka fara aiwatar da mafi karancin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan gwamnati.Ya kuma ce Bauchi ita ce jiha ta farko a Arewacin Nijeriya da ta fara aiwatar da mafi ƙarancin fansho na naira 32,000 ga ’yan fansho.Shi ma da yake magana a madadin shugabannin ƙananan hukumomi, Shugaban Karamar Hukumar Ningi, Alhaji Yahuza Adamu, ya ce biyan kuɗaɗen giratuti abu ne da zai iya farfaɗo da tattalin arzikin jihar.Yahuza ya ce biyan kuɗaɗen ya cika wani dogon buri da ’yan fansho suka daɗe suna jira, yana mai cewa gwamnatocin baya sun yi alƙawarin magance matsalar tarin bashin giratuti amma sun kasa.

Fansho
Khalid Idris Doya
+ postsBio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Bauchi Ta Yi Allah-wadai Da Kama Masu Kaɗa Ƙuri’a
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro
Manyan Labarai

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

September 23, 2026
An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano
Manyan Labarai

An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

September 23, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari
Manyan Labarai

Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

September 23, 2026
Next Post
Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

LABARAI MASU NASABA

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

Liu Guozhong Ya Halarci Shagulgulan Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin Na Bana

September 23, 2026
Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

Basukan Giratuti: Gwamnatin Bauchi Ta Fara N10bn Ga ‘Yan Fansho 1,700

September 23, 2026
Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

Sin Ta Yi Bikin Karrama ’Yan Sama Jannati Na Kumbunan Shenzhou-20 Da Shenzhou-21

September 23, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Ɗaga Albashin Sojoji Daga Naira 49,000 Zuwa Naira 100,000 – Ministan Tsaro

Ya Kamata Kowane Dan Nijeriya Ya Samu Horon Soja – Ministan Tsaro

September 23, 2026
Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

Yadda Fasahohin Noma Na Sin Ke Canza Rayuwar Manoman Afirka

September 23, 2026
An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

An Gano Jirgi Mara Matuƙi Da Ake Zargin Masu Laifi Na Amfani Da Shi A Iyakokin Kano

September 23, 2026
TMG Ta Buƙaci Atiku Da Obi Su Haɗa Kai Don Kayar Da Tinubu A 2027

TMG Ta Buƙaci Atiku Da Obi Su Haɗa Kai Don Kayar Da Tinubu A 2027

September 23, 2026
Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

Xi Jinping Ya Tashi Zuwa Amurka Don Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar

September 23, 2026
Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

Tinubu Ya Yi Wa Nijeriya Kyakkyawan Tanadi – Masari

September 23, 2026
Har Yanzu Tinubu Ne Ke Shugabancin Nijeriya Daga Waje – Akpabio

Har Yanzu Tinubu Ne Ke Shugabancin Nijeriya Daga Waje – Akpabio

September 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.