Wasu alkaluman haraji na baya bayan nan da aka fitar a jiya Litinin, sun nuna yadda kasar Sin ke samun karin karsashi a fannin samun sabon ikon sarrafa hajoji masu inganci cikin watanni takwas na farkon shekarar nan ta 2026, inda sassan sarrafa manyan kayayyakin fasaha da na fasahar AI ke kan gaba.
A cewar babbar hukumar haraji ta kasar Sin, daga watan Janairu zuwa Agustan bana, kudaden sayayyar hajojin masana’antun sarrafa manyan hajojin fasaha ya karu da kaso 15.7 bisa dari a mizanin shekara-shekara, yayin da sashen masana’antun ya samu ci gaban kaso 18.9 bisa dari.
Kazalika, kudaden shiga a bangaren sayayyar sassan harhada laturoni na IC masu nasaba da fasahar AI, da na na’urorin kera ababen hawa masu basira, suka samu karuwar kaso 67.7 da kaso 38.8 bisa dari a mizanin shekara-shekara. (Saminu Alhassan)













