Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya gargadi ’yan siyasa da masu rike da mukaman gwamnati da kada su dauki nauyin zuwa aikin Hajji ko ziyartar wuraren ibada a Makka da Kudus da kudaden gwamnati da aka wawure.
Sarkin ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na Majalisar Ƙoli ta Addinai ta Nijeriya (NIREC), da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.
Ya bukaci shugabannin addinai da su hada kai da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa domin dakile matsalar cin hanci a kasar.
Sarkin ya ce ba za a iya amfani da kudaden da aka samu ta hanyar cin hanci wajen gudanar da ibada ba, yana mai cewa Allah ba ya son cin hanci da rashawa.
Ya jaddada cewa satar kudi sannan a yi amfani da su wajen daukar nauyin mutane zuwa Makka ko Kudus ba zai sa aikin ya zama abin karɓa a wurin Allah ba.














