Xi Jinping Ya Halarci Taron Tunawa Da Cika Shekaru 90 Da Nasarar Doguwar Tafiya Tare Da Gabatar Da Jawabi
Xi Jinping Ya Halarci Taron Tunawa Da Cika Shekaru 90 Da Nasarar Doguwar Tafiya Tare Da Gabatar Da Jawabi Da safiyar yau, an gudanar da babban taron tunawa da cika shekaru 90 da nasarar doguwar tafiyar rundunar jajayen sojoji na ma’aikata da manoma karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin JKS a Beijing. Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS kana shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin koli na soja, ya gabatar da jawabi. A cikin jawabinsa Xi ya bayyana cewa, daga watan Oktoba na shekarar 1934 zuwa watan Oktoba na shekarar 1936, rundunar ta yi wata doguwar tafiya da ta girgiza duniya kuma ta shiga tarihi karkashin jagorancin JKS. Doguwar tafiyar rundunar sojin ta ratsa larduna sama da 10, ta kai km 12500, wadda ta dakile matakan da miliyoyin sojojin makiya suka yi na samame, matakin da ya sanar da gazawar makircin ‘yan adawar jam’iyyar Kuomingtang na dakile JKS da rundunarta. Ya jaddada cewa, ruhin doguwar tafiyar ya nuna karfin aminci da gaskiya, da karfin adalci da hadin kai, kuma a matsayinsa na muhimmin bangare na jerin ruhohin ‘yan JKS, dukiya ce mai daraja da ingantaccen karfi na karawa matasa kwarin gwiwa don su shawo kan kalubale da tafiya zuwa gaba. Xi ya kuma kara da cewa, tunawa da tarihi shi ne ginshigin kafa makoma, kuma ya kamata dukkan ‘yan jam’iyyar JKS da sojoji da dukkan al’ummar kasar su yayata ruhin babbar doguwar tafiyar, da ingiza babban aikin da magabata suka dukufa kan shi zuwa gaba. (Amina Xu)



















