Sin Na Adawa Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Kamfanoninta
Ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta ce, ci gaban da kamfanonin fasahar AI na kasar suka samu cikin sauri, ya samo asali ne daga lokaci mai tsawo da aka dauka ana zurfafa bincike mai tushe da kara karfin kirkire-kirkire, kuma ba shi da alaka da abin da ake kira wai “satar sirrin kasuwanci”. Kakakin ma’aikatar ne ya bayyana haka jiya Talata, yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan takunkumin da Amurka ta kakaba wa kamfanonin Sin bisa zargin satar sirrin kasuwanci. A cewar kakakin, Amurka na bata sunan kamfanonin Sin da kuma kakaba musu takunkumi, lamarin dake matukar lalata muhimmiyar moriyar kamfanonin, kuma Sin na adawa da hakan. Bugu da kari, game da sanarwar da ma’aikatar tsaron cikin gida ta Amurka ta fitar kan umarnin kayyadewa da hana shigar da kayayyakin kamfanonin Sin, kakakin ya ce, Sin na bukatar Amurka da ta mutunta tsari da ka’idojin kasuwa, kuma ta gyara kuskuren da take yi nan take, kana ta daina matsin lamba maras dalili kan kamfanonin Sin. Ban da wannan kuma, ta soke matakan nuna wariya, domin a shimfida kyakkyawan yanayi da kamfanonin kasashen biyu za su ci gaba da mu’amala da hadin gwiwa yadda ya kamata. Ya ce, Sin za ta ci gaba da lura da al’amarin, kuma za ta dauki duk matakan da suka dace kan duk wani abu dake lalata muradunta, don kare moriyar kamfanonin kasar. (Amina Xu)



















