Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya rushe kwamitin gudanarwar ƙungiyar kwallon ƙafa ta Wikki Tourists nan take, bayan rashin taɓuka...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya rushe kwamitin gudanarwar ƙungiyar kwallon ƙafa ta Wikki Tourists nan take, bayan rashin taɓuka...
Sake barkewar hare-hare tsakanin Amurka da Iran a ’yan kwanakin nan ya ja hankalin al’ummun duniya baki daya, tare da hasashen sake dandana mummunan tasirin da yakin zai haifar ga daukacin duniya baki daya idan har ya tsawaita. Duniya na fatan Amurka da Iran za su koma teburin shawarwari ba tare da bata lokaci ba, kana za su kai ga aiwatar da matakan dakatar da zubar da jini cikin hanzari, tare da taka wa yakin birki baki daya. Kasa da wata guda da cimma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran, a yanzu tashin hankalin na sake farfadowa. Mun dai ga yadda tun da sanyin safiyar ranar Talata, Amurka ta fara kaddamar da sabbin hare-hare kan sassan Iran cikin kwanaki uku a jere, yayin da ita ma Iran ke mayar da martani kan cibiyoyin aikin soji na Amurka dake kasashen yankinta. Sakamakon wannan dauki ba dadi, tuni farashin mai ya fara hauhawa, kura ta turnuke a mashigin Hormuz, kuma tsarin sufurin hajojin kasuwanci da ya yi matukar rauni a sakamakon tashin hankalin da ya gabata, a yanzu ma ya sake shiga yanayi na ha’ula’i. Masana da dama na cewa, Amurka da Iran ba za su mori wata fa’ida ba daga sake barkewar tashin hankali, kuma dukkanin kasashen duniya za su dandana kudarsu sakamakon sake barkewar tashin hankalin da ake gani a yanzu. Kafin cimma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin sassan biyu, mun ga yadda aka kai ruwa rana wajen tattaunawa, da tuntuba, da shiga tsakani na wasu sassa, har dai aka kai lokacin da Amurka da Iran suka sanar da kawo karshen yaki, da dakatar da daukacin ayyukan soji daga dukkanin fannoni, da kaucewa amfani da karfin soji ta kowane bangare. Sassan biyu sun kuma sha alwashin mutunta ikon mulkin kai da tsaron yankunan juna, tare da kaucewa tsoma hannu cikin harkokin gidan juna. Yanzu haka dai tasirin sake barkewar hare-hare tsakanin Amurka da Iran ya jefa farashin mai cikin yanayi na rashin tabbas, tare da sake gurgunta hada-hadar sufurin hajoji ta mashigin Hormuz, kuma hasashen baya bayan nan na asusun IMF ma, dangane da karuwar ci gaban tattalin arzikin duniya na bana ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, kasa da na watan Afirilun da ya shude, inda IMF din ya alakanta hakan kai tsaye da rikicin na gabas ta tsakiya. Alal hakika, duniya ba za ta yi farin ciki da dawowar yaki ba. Kuma sassan kasa da kasa na fatan sassan da rikicin ya shafa za su gaggauta komawa teburin shawarwari, maimakon dauki ba dadi da zai haifar da illa ga dukkanin bangarori. (Saminu Alhassan)
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Lin Jian, ya ce, dangane da babban taron fasahar AI na duniya da taron...
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika wa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, takardar tabbatar da shi a matsayin abokin...
Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev a birnin Shanghai, wanda ya zo kasar don halartar babban taron fasahar AI na duniya da taron manyan jami’ai na duniya kan tafiyar da sha’anin fasahar AI. Bayan ganawar, shugabannin kasashen biyu sun shaida sanya hannu tare da sanar da wasu takardu na hadin gwiwa a fannoni daban-daban, kamar tattalin arziki da ciniki, sufuri, har11kar kudi, da kuma kafofin watsa labarai. Da daren ranar, Xi Jinping da matarsa Peng Liyuan sun shirya wata liyafa a zauren liyafar duniya da ke Shanghai don maraba da manyan baki daga kasa da kasa da za su halarci bikin bude babban taron fasahar AI na duniya da taron manyan jami’ai na duniya kan tafiyar da sha’anin fasahar AI.(Safiyah Ma)
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Alhamis ya bukaci Rundunar Sojin Nijeriya da ta daina kallon aikinta a matsayin...
A yau Alhamis, an gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa kungiyar hadin gwiwar fasahar kirkirarriyar basira ta AI...
Jam'iyyar (ADC) ta sake shiga cikin rikicin cikin gida bayan daya daga cikin fitattun jagororinta, Salihu Mohammed Lukman, ya sanar...
A kwanan baya, kamfanin Nearpays na kasar Najeriya ya lashe kyaututtuka a Afirka da ma duniya baki daya, saboda manhajar biyan kudi ta wayar salula da ya tsara, wadda ta kunshi fasahar kirkirarriyar basira ko AI. Wani abu na musamman da ke cikin wannan manhajar shi ne yadda ya iya aiki ba tare da amfani da yanar gizo ko Intanet ba, wanda ke ba mutane damar biyan kudi ta wayar salula, ko da a yankunan karkara masu nisa inda ba a samun siginar wayar salula. Wannan hanyar amfani da fasaha wajen inganta rayuwar jama’a ta yi daidai da ka'idar amfani da fasahar AI ta Majalisar Dinkin Duniya ta "Fasaha mai fifita al’umma, amfani da AI ta hanyar da ta dace", kuma ra'ayi ne da kasar Sin ke kokarin aiwatarwa a fannin raya fasahar AI. A kasar Sin, babban burin da ake neman cimmawa ta hanyar amfani da fasahar AI shi ma ya kasance samar da hidimomi ga jama’a. Idan aka dauki misali da bangaren kula da lafiya, a wasu asibitoci na matakin unguwanni a birnin Beijing, na’urorin aiki masu kunshe da fasahar AI na iya taimaka wa marasa lafiya tsara shirin ganin likita, da tantance cututtukan ido, da kuma taimaka wa likitoci wajen neman bayanan tarihin jinya, da tantance hotunan da aka dauka ta na’urorin bincike, da kuma kula da magunguna. Ta wannan hanya, an daidaita aikin jinya a asibitocin, da kuma samar da sauki ga marasa lafiya. A zahiri, "Dora mihimmanci kan moriyar jama’a" wani tunani ne na bai daya na Sin da Afirka ta fuskar fasahar AI. Sai dai mabambantan kasashe su kan samu ra’ayoyi masu bambanci. Misali, yanayin da ake ciki a Amurka ya bambanta. Cikin wata makalar da ya rubuta, masanin ilimin al’amuran duniya dan kasar Kenya Elijah Mwangi ya bayyana bambanci da ke tsakanin salon kasar Sin da na Amurka a fannin raya fasahar AI. Ya bayyana cewa dabarar raya fasahar AI ta Sin ta shafi manufar sanya gwamnati ta rika ba da jagoranci, da kokarin samar da na’urorin zamani a matsayin ababen more rayuwa, yayin da Amurka ke bin tsarin jari-hujja. Wato masana'antun fasahar AI na Amurka galibinsu manyan kamfanoni ne ke kula da su bisa tsarin kasuwanci. A ganin wadannan kamfanoni, damar samun riba da takara da kamfanonin sauran kasashe, sun fi bauta wa jama’a muhimmanci. Idan aka dauki fannin kiwon lafiya a matsayin misali, Amurka tana kokarin amfani da fasahar AI wajen inganta wani tsarin kiwon lafiya mai tsada, maimakon bai wa talakawa damar samun hidimomi masu araha. Wannan babban bambanci ne ya sa kasar Sin fara gabatar da manufar kula da ayyukan raya fasahar AI mai amfanar da al’ummun duniya, wadda ta kunshi ra’ayoyin "Raya fasahar AI don samar da alfanu, da tsaro, da adalci", da "Ba da taimako ga kasashe masu tasowa" , da "Tabbatar da wakilcin kasashe masu tasowa a fannin kula da fasahar AI", da sauransu. Daga gabatar da "Shawarar kula da harkoki masu alaka da fasahar AI na duniya" , zuwa aiwatar da "Shirin raya fasahar AI mai amfanar da kowa", kasar Sin tana kokarin mai da fasahar AI wani lamari da zai amfanar da dukkan bil'adama. A lokacin da ake magana kan fasahar AI ta kasar Sin, masana ilimin kimiyya da fasaha ’ya’yan Afirka su kan yaba mata bisa yadda take da araha. Elijah Mwangi ya ce, karfin kasar Sin a fannin kera kayayyaki, ya sanya ta zama bangare mai muhimmanci dake samar da hidimomi masu araha ga masu amfani da fasahar AI. Wannan ya saukaka wa kasashen da ke son amfani da fasahohin zamani kuma a farashi mai rahusa. A nasa bangare, Lawrence Nderu, wani shehun malami dake aiki a jami'ar kimiyya da fasaha masu alaka da aikin gona ta Jomo Kenyatta ta kasar Kenya, ya yaba wa manhajojin fasahar AI na kasar Sin, wadanda suka zama “Open Source”, wato nuna dukkan bayanan tsara manhaja ba tare da boye su ba. Ya ce bisa amfani da wadannan manhajojin kasar Sin, kungiyoyi masu tsara manhaja na kasashen Afirka za su iya kara dogaro da kai, da kare bayanai masu mahimmanci, da kuma samar da dabarun daidaita matsalolin da ake fuskanta a kasashen Afirka. Yadda ake amincewa da tunani da fasahohi masu nasaba da AI na kasar Sin shi ma ya inganta hadin gwiwar Sin da Afirka. A Afirka ta Kudu, kamfanonin kasar Sin sun ba da taimako wajen daidaita tsarin kula da zirga-zirgar jiragen kasa, wanda ya tabbatar da tsaro. A Djibouti, tsarin ba da gargadi don kandagarkin bala’i na "MAZU-Urban", wanda hukumar kula da ayyuka masa alaka da yanayi ta kasar Sin ta bayar kyauta, ya taimaka wajen rage mummunan tasirin bala’i daga Indallahi ga tattalin arziki da rayuwar mutane. Wadannan lamuran sun nuna cewa "dora muhimmanci kan moriyar jama’a" ra’ayi ne na bai daya na Sin da Afirka dagane da aikin raya fasahar AI. Bugu da kari, wannan ra’ayin ya tabbatar da kyakkyawar makoma ga yunkurin zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. (Bello Wang)
Sakamakon wani binciken da kafar yada labarai ta CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ta...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.