ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Zan Iya Jure Halayen El-Rufai Ba Shi Yasa Na Fice Daga ADC – Salihu Lukman

by Sulaiman and Shehu Yahaya
2 months ago
ADC

Jam’iyyar (ADC) ta sake shiga cikin rikicin cikin gida bayan daya daga cikin fitattun jagororinta, Salihu Mohammed Lukman, ya sanar da dakatar da kasancewarsa a jam’iyyar da kuma gamayyar jam’iyyun adawa, inda ya zargi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da haddasa wulakanci da ware shi daga harkokin jam’iyyar.

A cikin wata sanarwa da ya aikewa Shugaban ADC na kasa, Sanata David Mark, tare da kwafin ga shugabannin gamayyar adawa, Lukman ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan watanni na abin da ya kira ci gaba da cin zarafinsa da kuma nuna masa wariya daga El-Rufai da wasu na kusa da shi kan yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar a Jihar Kaduna.

Lukman ya ce ya yi hakuri na tsawon lokaci, amma ya kasa ci gaba da jure irin yadda ake mu’amala da shi.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Ina matukar bakin ciki da wannan mataki, amma ba zan iya ci gaba da jure irin wulakancin da nake fuskanta daga wasu shugabannin Kaduna ba, musamman Malam Nasir El-Rufai.”

Ya kuma yi zargin cewa ana karkatar da yanke hukunci kan wakilcin shugabanci a Kaduna domin a mayar da shi saniyar ware, yana mai cewa an rage darajarsa duk da irin kokarin da ya yi wajen kafa da hada kan gamayyar jam’iyyun adawa.

LABARAI MASU NASABA

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Tsohon Mataimakin Shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma ya bayyana cewa ya shafe sama da shekara guda yana kokarin sasanta shugabannin adawa a Kaduna tare da gina ADC, amma a maimakon a yaba masa sai aka mayar da shi abin hari.

Lukman ya ce saboda hakan ya yanke shawarar dakatar da kasancewarsa a ADC da kuma gamayyar jam’iyyun adawa, yana mai cewa gara ya dakata da harkokin siyasa na wani lokaci fiye da ci gaba da bin abin da ya kira “burin da ya rushe.”

Har ila yau, ya zargi wasu shugabannin gamayyar da rashin bin ka’idojin dimokuradiyya, yana mai cewa suna maimaita irin salon siyasar da suka dade suna suka, wanda ya janyo matsaloli a jam’iyyunsu na baya.

Lukman ya yi zargin cewa tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, na tuntubar wasu mutane a Kaduna da, a cewarsa, ba su da cikakkiyar niyyar gina ADC, tare da yin watsi da wadanda suka sadaukar da lokacinsu wajen karfafa jam’iyyar.

ADC
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina Kasa
ADC
Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden

MASU ALAKA

Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia
Manyan Labarai

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato
Manyan Labarai

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Next Post
An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

An Yi Bikin Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Kafa Kungiyar Hadin Gwiwar Fasahar AI Ta Duniya A Shanghai

LABARAI MASU NASABA

ADC

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.