Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Alhamis ya bukaci Rundunar Sojin Nijeriya da ta daina kallon aikinta a matsayin aikin wanzar da zaman lafiya ko kwantar da tarzoma kawai, inda ya ce ya kamata ta dauki yawaitar kashe-kashe a Filato da sauran yankunan da ke fama da matsalar tsaro a matsayin barazana ga ‘yancin kasa.
Mutfwang ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin Babban Kwamandan Runduna ta 3 ta Sojin Nijeriya kuma Kwamandan Operation Safe Haven, Manjo Janar Folusho Oyinlola mai barin gado, tare da magajinsa, Manjo Janar Williams Dangana, a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Jos.
Gwamnan ya ce kalubalen tsaro da ke addabar Jihar Filato da yankunan Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na bukatar daukar matakan soja masu tsauri da inganci.













