ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
2 months ago
Wikki

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya rushe kwamitin gudanarwar ƙungiyar kwallon ƙafa ta Wikki Tourists nan take, bayan rashin taɓuka abun arziki da ƙungiyar ta yi a kakar wasan 2025/2026 ta Gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL), wanda ya janyo faɗuwarta zuwa Gasar Nijeriya ta NNL.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar a daren ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnan ya amince da rushe kwamitin ne bayan nazari mai zurfi kan yadda ƙungiyar ta taka leda a kakar wasa da kuma matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin tabbatar da ta ci gaba da kasancewa a babbar gasar kwallon kafa ta ƙasar.

ADVERTISEMENT

Ya ce wannan mataki na nuna kudirin gwamnatin jihar na sake farfaɗo da Wikki Tourists, dawo da amincewar jama’a kan yadda ake tafiyar da ƙungiyar, tare da shimfiɗa ingantaccen tubali domin dawowarta cikin gaggawa zuwa babbar gasar kwallon kafa ta Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a tsawon kakar wasan, gwamnatin jihar ta bai wa ƙungiyar dukkanin tallafin kuɗi da na gudanarwa da ake buƙata domin kara mata karfin gasa da inganta kwazonzo, amma kash sai ta Ka-sa-ka-sau.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, a matsayin matakin ƙarshe na ƙoƙarin kauce wa faɗuwa daga gasar, gwamnati ta kafa Kwamitin Ceto (Rescue Team) a karshen kakar wasan domin ya haɗa kai da kwamitin gudanarwa wajen ceto ƙungiyar.

“Abin takaici, duk da waɗannan matakai, ba a samu sakamakon da ake buƙata ba, inda daga ƙarshe ƙungiyar ta fadi zuwa Gasar Nijeriya ta kasa (NNL),” in ji sanarwar.

Saboda haka, Gwamna Bala Mohammed ya amince da naɗin tsohon daraktan wasanni na Jihar Bauchi, Alhaji Haruna Bako, a matsayin mai kula da ƙungiyar na wucin hadi (Interim Sole Administrator), har sai an kafa sabon kwamitin gudanarwa na dindindin.

Sanarwar ta ce ana sa ran sabon mai kula da ƙungiyar zai karɓi ragamar gudanarwa nan take, amsar ragamar kula da dukkan ayyuka, ƙadarori, takardu da kuma alhakin ƙungiyar, tare da fara ɗaukar matakan da za su sake farfaɗo da ƙungiyar domin samun kyakkyawan sakamako da kuma shiri mai inganci a kakar Gasar Nijeriya ta ƙasa mai zuwa.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta kuma nuna godiyarta ga kwamitin gudanarwar da aka kora ƙarƙashin jagorancin Salmanu Abubakar bisa gudummawar da ya bayar ga ƙungiyar, tare da yi musu fatan alheri a dukkan ayyukansu na gaba.

Gwamnatin ta sake jaddada ƙudirinta na farfaɗo da Kungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourists, tana mai tabbatar wa magoya bayanta cewa za a ɗauki dukkan matakan da suka dace domin mayar da kungiyar cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na Nijeriya da kuma tabbatar da dawowarta cikin gaggawa zuwa Gasar Firimiya ta Nijeriya (NPFL).

Wikki
Khalid Idris Doya
+ posts Bio
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Yaro Ya Harbe Kansa Har Lahira Bayan Mafarauci Ya Yi Sakaci Da Bindigarsa A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    An Kama Mutane 5 Da Sassan Jikin Ɗan’Adam Za Su Yi Tsafi A Bauchi
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan Bauchi, Bala Jibrin, Ya Fice Daga APC Kan Zargin Ɗoki-ɗora
  • Khalid Idris Doya
    https://hausa.leadership.ng/author/khalid-idris-doya/
    ‘Yansanda Sun Cafke Tsoho Mai Shekara 70 Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 8 Fyaɗe A Bauchi
Wikki
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.