ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Bankin Duniya ya bayyana damuwa kan yadda kashi 79 cikin 100 na ƴan Nijeriya har yanzu ke rayuwa cikin talauci ko kuma ke cikin haɗarin faɗawa cikin talauci duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin tarayya ta ke aiwatarwa kusan shekaru uku da suka gabata.

Bankin ya ce samar da ayyukan yi shi ne babbar hanyar da za ta fitar da miliyoyin ƴan Nijeriya daga ƙangin talauci, kamar yadda ya bayyana a cikin Tsarin Haɗin Gwuiwa da Nijeriya (Country Partnership Framework – CPF) na 2026 zuwa 2032.

Rahoton ya nuna cewa kashi 33 cikin 100 na ƴan Nijeriya na rayuwa cikin matsanancin talauci, wato ba sa iya biyan mafi ƙarancin buƙatun abinci, yayin da kashi 61 cikin 100 ke rayuwa ƙasa da layin talauci na ƙasa da aka shata.

ADVERTISEMENT

Bankin ya ƙiyasta cewa kimanin mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci a Nijeriya, musamman a jihohi Arewa.

Rahoton ya kuma bayyana cewa sama da mutane miliyan 86 ba su da wutar lantarki, yayin da matasa tsakanin miliyan uku zuwa huɗu ke kai wa matsayin fara neman aiki a kowace shekara ba tare da isassun damar samun aikin yi ba.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Bankin Duniya ya amince cewa wasu sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar, ciki har da cire tallafin fetur, da sassauta tsarin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, da tsaurara manufofin kuɗi da sauye-sauyen haraji, sun taimaka wajen daidaita tattalin arziƙi da ƙara amincewar masu zuba jari.

Rahoton ya ce bunƙasar tattalin arziƙin ƙasar ta ƙaru daga kashi 3.5 cikin 100 a farkon rabin shekarar 2024 zuwa kashi 3.9 cikin 100 a daidai wannan lokaci na shekarar 2025, Yayin da ajiyar kuɗaɗen waje ta haura dala biliyan 42.

Sai dai Bankin ya gargaɗi cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da rage ƙarfin sayen al’umma, musamman masu ƙaramin ƙarfi, yayin da shirye-shiryen tallafin jin daɗin jama’a ke tafiya a hankali.

Haka kuma, ya ce raunin hukumomi, da rashin ingantaccen haɗin gwuiwa wajen aiwatar da manufofi da ƙarancin gaskiya wajen tafiyar da kasafin kuɗi na daga cikin manyan ƙalubalen da ke iya hana tattalin arziƙin Nijeriya samun cikakkiyar farfaɗowa.

Bankin ya jaddada cewa ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙi tare da ƙarin gyare-gyaren tsari zai zama wajibi domin inganta rayuwar ƴan Nijeriya a nan gaba.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Ra’yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

Ra'yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.