Marafa Ya Yi Alƙawarin Murabus Idan Ya Kasa Magance Tsaro Cikin Shekaru Biyu
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya yi alkawarin cewa zai yi murabus idan aka...
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya yi alkawarin cewa zai yi murabus idan aka...
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani shahararren mai ƙirƙirar bidiyo a TikTok, Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani...
Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai shiga tsakani domin sasanta rikicin siyasa da ya kunno kai tsakanin...
Rundunar ’Yansandan Jihar Katsina ta dakile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Dutsin-Ma, tare da ceto mutane huɗu da...
Tsohuwar uwargidan Shugaban Nijeriya, Aisha Buhari, ta ziyarci tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar. Atiku ne ya bayyana hakan a...
Yayin da yanayin duniya ke cike da sauye-sauye da tashe-tashen hankali, gibin tsaro na kara haifar da damuwa. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya, ya nuna kaso 89.6 na masu bayar da amsa na kira ga dukkan kasashe su warware takkadama a tsakanin su ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa. Yayin da kaso 80.4 na masu bayar da amsa daga kasashe masu tasowa suka bayyana cewa, dabi’ar yakin cacar baka da neman iko, na barazana ga zaman lafiya a duniya da kara kalubalen tsaro, suna masu kira ga dukkan kasashe su hada hannu wajen samar da tsarin tsaro mai inganci da daidaito da dorewa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya a New York, inda zai gana da shugabannin...
A jiya Talata ne mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya gabatar da jawabi, a liyafar da aka shirya don nuna maraba da baki mahalarta taron dandalin tattaunawa na Xiangshan da ake gudanarwa kan sha’anin tsaro a birnin Beijing karo na 13, inda wakilai daga kasashe da yankuna da kuma kungiyoyin duniya kusan 100 suka halarta. A jawabin da ya gabtar, ya ce duk da kalubalen da duniya ke fuskanta a halin yanzu, manufar samar da zaman lafiya, bunkasa ci gaba, hadin gwiwar kasashe, da samun nasara ga kowane bangare, abu ne da ba za a iya dakatar da shi ba, sannan babu ja da baya kan yanayin da ake ciki na samun bunkasar kasashe daban daban da dunkulewar tattalin arzikin duniya wuri guda. Han Zheng ya jaddada bukatar kiyaye manufofi da dokokin MDD, da tsayawa kan ingantaccen tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa da tuntubar juna, sanya bukatar al’umma a gaba da kome, da kuma tabbatar da cewa fasahohi sun zama abin moriya ga cigaban dan Adam. Ya kara da cewa a a matsayin Sin na babbar kasa kuma kasa mai tasowa mafi girma a duniya, a kullum tana sanya ci gabanta ne domin bunkasa rayuwar dan Adam, da kuma ba da gudunmawarta domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da kuma ci gaba ta hanyar zamanantar da kanta. Har ila yau, yayin da ake bikin bude taron dandalin Xiangshan na Beijing karo na 13 a yau Laraba, minitan tsaron kasar Sin, Dong Jun ya jaddada batun kiyaye kwanciyar hankali a bisa tsarin mabambantan bangarori. Dong ya yi kira da a ci gaba da yin riko da tsarin mabambantan bangarori na hakika, da kafe kai da fata wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin MDD, da kuma tsarin duniya da aka shimfida bisa dokokin kasa da kasa. Kazalika, Dong ya jaddada bukatar sanya darussan da aka koya daga tarihi a cikin zukata da ci gaba da sa-ido sosai game da babakeren wata kasa, da tara karfin soji da kuma maimaita tarihi. Dong ya yi nuni da cewa, darussa masu daci da aka koya daga yake-yaken duniya da bala’o’in rikice-rikice da hargitsin da ake fama da su a yau, suna gargadi ne kan cewa rigakafin barkewar rikici dabara ce mafi muhimmanci a bangaren tafiyar da sha’anin tsaro.
Dakarun haɗin gwiwar rundunar tsaron Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun hallaka wasu ’yan ta’adda biyu, ciki har da...
Da safiyar yau 16 ga watan nan, jami'in farko na gwamnatin yankin musamman na Hong Kong Lee Ka Chiu John ya gabatar da shirin shekaru 5 na farko na raya yankin musamman na Hong Kong ga hukumar kafa dokokin yankin, inda ya bayyana cewa, shi ne karon farko da aka gabatar da shirin, kuma ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Sin ta fara aiwatar da shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Sin na shakaru biyar-biyar karo na 15. A cewarsa, wannan wani mataki ne da gwamnatin yankin Hong Kong ke dauka don kama hanya iri daya tare da gwamnatin tsakiyar kasar, da kuma shiga a dama da ita don tabbatar da bin tsarin ci gaban kasa yadda ya kamata, kana da kaiwa ga matsaya daya tsakanin al'umma da karfafa hadin gwiwar mabambantan bangarori, ta yadda za a ciyar da Hong Kong gaba daga kwanciyar hankali zuwa samun wadata, da kuma cimma ingantaccen ci gaba. Lee Ka Chiu John ya ce, an kama hanya mafi dacewa ta samun ci gaba da rarraba albarkatu yadda ya kamata da kuma tabbatar da kwanciyar hankalin al’umma a dogon lokaci, da ba da tabbaci ga jin dadin mazauna da muradun masu zuba jari na wurare daban-daban, bisa shirin na shekaru 5. Dadin dadawa, za a kara raya yankin Hong Kong bsia tsarin bude kofa ga ketare da amfanarwa ga kowa, kuma cikin ’yanci da adalci da wadata da tsaro, inda hakan zai sa yankin Hong Kong ya zama mahadar Sin da duniya, da kuma zama yanki mai jawo hankalin kasa da kasa da zai kasance cike da kuzari da damammaki. (Amina Xu)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.