Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani shahararren mai ƙirƙirar bidiyo a TikTok, Ukasha Yahaya, wanda aka fi sani da “UK International”, bisa zargin wallafa bidiyoyin da ke nuna shi tare da mata cikin abubuwan da hukumar ta bayyana a matsayin rashin da’a.
Mataimakin Shugaban Kwamandan Hukumar, Dr. Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar da kama matashin mai shekaru 27 a ranar Alhamis, inda ya ce an kama shi ne bayan hukumar ta samu bayanan sirri cewa ya shigo Kano.
Aminuddeen ya ce Ukasha na tsare a hannun hukumar yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.
A yayin bincike, Ukasha, wanda dan asalin Gusau ne a Jihar Zamfara kuma mazaunin Abuja, ya ce ba zai iya tuna adadin bidiyon da ya shirya tare da mata ba. Ya kuma bayyana cewa wasu daga cikin bidiyoyin nasa sun samu kallo tsakanin miliyan daya zuwa uku.
Mai TikTok din ya nemi afuwa tare da alkawarin ba zai sake aikata irin hakan ba, yana kuma cewa yana tunanin daina irin wadannan bidiyoyi yayin da yake shirin yin aure.
Binciken da Daily Trust ta gudanar, ya nuna cewa, shafinsa na TikTok mai suna “UK INTERNATIONAL” na da mabiya sama da 262,000, yayin da bidiyoyinsa suka samu jimillar ‘likes’ miliyan 2.4.













