ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

by Sulaiman
46 seconds ago
APC

Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai shiga tsakani domin sasanta rikicin siyasa da ya kunno kai tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da wasu gwamnonin da aka zaɓa ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan Gwamnonin APC, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC (PGF), Gwamnan Imo Hope Uzodimma, sun bayyana cewa ba za su goyi bayan wata ƙawance ko tsarin siyasa da zai raunana APC ko ’yan takararta a zaɓen 2027 ba. 

Wannan matsaya ta zo ne yayin da Wike ke ƙarfafa shirin kawancen jam’iyyun mai taken “Rainbow Coalition”, wata ƙungiyar siyasa da ya ce manufarta ita ce tattara goyon bayan sake zaɓen Tinubu, ba tare da hana PDP da sauran jam’iyyun siyasa tsayar da ’yan takara a sauran kujerun zaɓe ba. 

ADVERTISEMENT

Wike ya kuma bayyana cewa goyon bayansa ga Tinubu ba yana nufin ya fice daga PDP ko kuma ya goyi bayan dukkan ’yan takarar APC ba. Ya ce yana da ’yancin tallafa wa ’yan takarar da ya zaɓa a sauran zaɓukan.

A cewar rahotannin siyasa, ana sa ran Tinubu zai gana da mambobin PGF bayan dawowarsa Nijeriya daga Turai domin tattauna matsalar da kuma neman hanyar sasanta ɓangarorin.

LABARAI MASU NASABA

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

Wasu rahotanni sun kuma ce Wike, wanda ke Spain a halin yanzu, na iya ganawa da Tinubu a Faransa kafin Shugaban Ƙasar ya dawo Nijeriya.

Wike ya ce Shugaban Ƙasa yana sane da ayyukan “Rainbow Coalition” ɗinsa, yayin da gwamnonin APC ke ganin cewa irin wannan tsarin na iya haifar da rabuwar kai a tsakanin ’yan jam’iyyar da kuma ’yan takararta. 

Rikicin ya zo ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen zaɓen 2027, musamman kan yadda za a haɗa goyon bayan siyasa ga takarar shugaban ƙasa da kuma ’yan takarar gwamna da ’yan majalisu a jihohi daban-daban.

APC
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    ’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina
  • Sulaiman
    Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku
  • Sulaiman
    Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa
  • Sulaiman
    Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

MASU ALAKA

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku
Manyan Labarai

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

September 17, 2026
Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 
Manyan Labarai

Gwamnan Kano Ya Naɗa Hafsat Kutama Mukaddashiyar Shugabar Hukumar PCACC 

September 16, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Sama Da 1,100 Cikin Shekara Ɗaya – Kwamanda

September 16, 2026

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

Tinubu Zai Shiga Tsakani A Rikicin Wike Da Gwamnonin APC

September 17, 2026
Kawayen amarya

’Yansanda Sun Ceto Mutane, Sun Daƙile Harin ’Yan Bindiga A Katsina

September 17, 2026
Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

Aisha Buhari Ta Ziyarci Atiku

September 17, 2026
Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

Nazarin CGTN: Dole Ne Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Samar Da Tsaro Mai Dorewa

September 16, 2026
Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

Haɓaka Tattalin Arzikin Zamfara: Gwamna Lawal Zai Halarci Babban Taron MDD A New York

September 16, 2026
Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Taron Dandalin Xiangshan Da Ake Gudanarwa Kan Sha’anin Tsaro A Beijing

September 16, 2026
Wani Mai Taɓin Ƙwaƙwalwa Ya Kashe Soja A Legas

Sojoji Sun Hallaka Wani Jagoran ’Yan Ta’adda A Katsina

September 16, 2026
Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

Lee Ka Chiu: Shirin Shekaru 5 Na Farko Na Raya Yankin Musamman Na Hong Kong Ya Dace Da Muradun Kasar Sin

September 16, 2026
Gwamnatinmu Za Ta Kawar Da Talauci Da Zarar An Zabe Mu – Shettima

Gwamnonin Arewa 6 Kacal Ne Suka Goyi Bayan Tinubu A 2023 – Shettima

September 16, 2026
Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN

Hanyar Ruwa Ta pinglu Ta Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN

September 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.