Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Zamfara, Sanata Kabiru Marafa, ya yi alkawarin cewa zai yi murabus idan aka zabe shi gwamna kuma ya kasa cimma akalla kashi 75 cikin 100 na manufofinsa na magance matsalar tsaro cikin shekaru biyu.
Marafa ya bayyana hakan ne a Gusau yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce burinsa na tsayawa takara shi ne bayar da gudummawa wajen dawo da zaman lafiya da ci gaba a jihar.
Ya ce ba zai bayyana cikakkun dabarun tsaron da yake shirin amfani da su ba har sai an zabe shi tare da rantsar da shi, amma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta fara aiki kan matsalar tsaro tun daga farkon wa’adinta.
Dan takarar ya kuma bayyana cewa yakin neman zabensa zai mayar da hankali kan tuntubar masu ruwa da tsaki da mazauna jihar domin gano matsalolinsu da karfafa tsarin jam’iyyar gabanin zabe.













