An Bude Taron Kasa Da Kasa Karo Na 5 Dangane Da Tsarin Cin Gajiyar Fasahar Taurarin Dan Adam Na Beidou
A yau Talata ne aka bude taron karawa juna sani na kasa da kasa karo 5, dangane da tsarin cin gajiyar fasahar taurarin dan’adam na BeiDou, a birnin Zhuzhou na lardin Hunan. Mataimakin firaministan kasar Sin Zhang Guoqing, ya halarci bikin bude taron ya kuma gabatar da jawabi. A cikin jawabin nasa, Zhang Guoqing ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkanin sassa, wajen kara inganta kirkire-kirkiren fasaha a tsarin aikin taurarin bayar da jagorancin taswira na BeiDou, da karfafa hade tsarin na BeiDou da fasahohi irinsu AI, da taurarin dan’adam na intanet, da kyautata tsarin jagorancin duniya mai nasaba da zayagen taurarin dan’adam, ta yadda hakan zai baiwa tsarin aikin BeiDou damar inganta hidimomin da yake baiwa duniya, da amfanar da daukacin bil’adama. Gabanin bude taron, Zhang Guoqing ya gana da firaministan kasar Madagascar Mamitiana Rajaonarison, wanda ya halarci taron. Taron na wannan karo na da taken "BeiDou domin duniya-Karfafa ci gaban duniya." Ya kuma hallara baki kimanin 900, ciki har da kwararru da masana, da manyan ‘yan kasuwa, da jami’an gwamnatoci na Sin da na kasashen ketare, da wakilan hukumomin kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)



















