Kasar Sin ta yi nasarar harba taurarin dan’adam na ayyukan sadarwar intanet guda 10, ta amfani da rokar Zhuque-2E Y7, daga cibiyar harba kumbuna ta Dongfeng dake arewa maso yammacin kasar.
An harba taurarin dan’adam din ne da karfe biyu da mintuna 26 na tsakar ranar yau Talata, kuma za su yi aiki tare da dandazon taurarin dan’adam na hidimomin sadarwar intanet, sun kuma shiga da’irorin da aka tsaya yadda ya kamata.
An dai ayyana cimma cikakkiyar nasara a aikin harba taurarin dan’adam din na wannan karo. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














