Shalƙwatar tsaron ta ƙasa (DHQ) ta ƙaryata rahotannin da ke cewa an samu wata sabuwar ƙungiyar ƴan ta’adda mai suna Fethulla (FETO) a Nijeriya.
Daraktan hulɗa da Jama’a na rundunar tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan a yau Alhamis, inda ya jaddada cewa Nijeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yanci wadda ke da ikon yanke shawara kan harkokin tsaro da yaƙi da ta’addanci.
- Fasahar Amfani Da ’Yan Sandan Mutum-Mutumi Ta Kasar Sin Na Iya Taimaka Wa Tsaro A Afirka
- Taron Matasan Sin Da Afrika Kan Tsaro Zai Kirkiro Wata Sabuwar Mahanga Ta Magance Matsalolin Tsaro
Wannan martanin ya biyo bayan jawabin da gwamnatin Turkiyya ta yi, inda ta zargi cewa mambobin ƙungiyar da take kira FETO na aiki a Nijeriya ta hanyar kafa cibiyoyin ilimi da lafiya.
Sai dai a martaninsa, Janar Kangye ya ce babu wani sahihin bayani daga hukumomin tsaro na Nijeriya da ke tabbatar da wannan zargi, yana mai cewa “kowa na da ‘yancin faɗin albarkacin bakinsa, amma hakan ba yana nufin hakan gaskiya ba.”
Ya ƙara da cewa Nijeriya ba za ta karɓi duk wata magana daga ƙasashen waje ba tare da sahihiyar bincike da tantancewa daga hukumominta ba, domin ita ƙasa ce mai cikakken ikon kanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp