Dan majalisar dokikin Jihar Kaduna kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin wucin gadi da ke bincikar tsohuwar gwamnatin Jihar Kaduna, Honorabul Mahmoud Lawal Isma’la, ya bayyana cewa bisa samun gamsassan bayanai kan yadda tsohuwar gwamnatin jihar ta karkatar da kudaden jihar ya sa ba su gayyaci Nasiru el-Rufai ba, domin gurfana a gaban kwamitin binciken.
Honorabul Lawal wanda aka fi sani da Bola Ige, ya ce kwamitinsu ya gano cewa daga shekarar 2015 zuwa 2023, Jihar Kaduna ta samu kudaden tallafi daga wajen jihar na naira tiriliyan 3, amma ba su san abin da aka yi da su ba, baya ga bashin ‘yan kwangila da suke bin gwamnatin na naira biliyan 311, sabanin yadda tsohuwar gwamnatin ta ce bashin ‘yan kwangilan na naira biliyan 115 ne.
- Wakilin Sin Ya Yi Bayani Kan Matsayin Sin Kan Kare Hakkin Dan Adam
- HOTUNA: Zanga-zanga Ta Barke A Kaduna Kan Bukatar Gurfanar Da El-Rufai
Dan majalisar ya bayyana haka ne a bayyana haka ne a cikin Shirin Barka Da Hantsi Nijeriya na LEADERSHIP Hausa da ake gabatarwa kai-tsaye a shafukan sadarwar zamani daga ranakun Litinin zuwa Juma’a da misalin karfe 9 na safe. Inda ya kara da cewa, yadda aka yi wasa da dukiyar al’ummar Jihar Kaduna abin ya wuce misali.
“Dalilin da sanya ba mu gayyaci el-rufai ba shi ne, duk abin da za mu tambaye shi mutanan da muka gayyata sun ba mu amsarsu, saboda haka sai muka ga ba ma bukatar gyayatarsa.
“Akwai kuma wata takarda da el-rufai ya rubuta ya ce ya dakatar da hukumar da take tsarawa da ba da kwangila ta Jihar Kaduna (KADPPA), daga ba da duk wata kwangila, haka kuma ya cire hannunsa daga ba da kwangila a jihar. Wannan takarda ita kadai ta wadatar da kwamitinmu. Haka kuma duk wata takarda da ta shafi kudin ‘yan kwangila ita ce ta zame mana jagora.
“Akwai kwamishinan el-rufai da ya ce duk bashin da aka ci babu amincewar majalisar tarayya wanda hakan ya saba wa dokar kabar bashin kasashen waje.
“Hadimin el-Rufai, Jimmy Lawal, da muka gayyata ya ce ba zai iya yin magana kan bashin da el-Rufai ya ci ba, abin da ya sani shi ne, lolacin da aka ciwo bashin majalisa ba ta zauna ba. Saboda haka duk abin da ya kamata mu ji daga bakin el-Rufai kwamishinoninsa sun fayyace mana.
“Akwai kwamishinan kudin el-Rufai ya tabbatar mana da cewa duk kudaden da aka karba domin a yi aiki tun kamin kudin su zo an riga an yi aikin, saboda haka da zarar kudin sun zo sai a karkatar da su zuwa wani wurin.”
Ya ci gaba da cewa tsohuwar gwamnati ta ce ta biya ‘yan kwangila naira biliyan 36, wanda kudin ya fi karfin aikin da suka yi, lamarin da ya sanya kwamitin suka zagaya duk inda aka bayar da aikin domin tabbatar da halin da ake ciki.
A cewarsa, kudin da aka biya ‘yan kwangila na nunka aikin da suka yi sau uku.
“A takarar barin gwamnati da el-Rufai ya bai wa Gwamna Uba Sani ya nuna cewa naira biliyan 115 ‘yan kwangila suke bin gwamnati, amma da muka bincika sai muka ga kudin ya haura haka ya kai naira biliyan 311, daga ciki an biya su naira biliyan 200, kuma ba su yi aikin da ya kai haka ba. Duk kwangilar da ka bayar akwai wadanda an kara musu kudin aikin, wasu kuma ba su yi aikin ba, yayin da wasu sun fara aikin sun bari, saboda haka duk bashin da aka karbo a Jihar Kaduna an karbo ne ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.
Ya ce kwamitin ba shi da niyyar cin mutuncin wani ko muzanta wani ba, yana mai cewa, “Tun lokacin da muka fara aikin, gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani bai taba kiranmu ba, hasalima bai san halin da kwamitin yake ciki ba, saboda babu hannunsa a cikin aikin kwamitinmu.
“Bukatar kwamitinmu shi ne, a dawo da makudan kudaden da aka sace domin yi wa al’ummar Jihar Kaduna aiki da su.” Ya bukaci al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba bai wa gwamnati goyon baya wajen ganin an kara samun ayyukan ci gaba a fadin jihar baki daya.