El-Mansur Abubakar" />

Badakalar EFCC: Cire Ibrahim Magu Ba Zai Kawo Sauyi Ba 

Alhaji Babangida Usman dan Malikin Progress FM Gombe, ya ce zargin cin hanci da rashawa da ta sa aka  cire Ibrahim Musthapha Magu, ba zai kawo sauyi ba, dalili kuwa shi ne duk ‘yan Nijeriya halin mu iri daya ne.

Babangida Usman, ya ce Ibrahim Magu da farkon zuwan sa EFCC ba haka aka yi tsammani daga wajen sa ba, saboda yadda yake bai wa ‘Yan Nijeriya tsoro wajen jajircewa da yaki da karbar rashawa sai ga yadda karshen ta zo, ban yi mamaki ba saboda idan aka bi ta barawo a bi ta mabi sawu.

Ya ce canji ake tsammani daga wajen sa kamar yadda ya faro da farko sai ga shi ya yi karkon kifi, amma dai ba shi kadai yake da laifi ba domin shi ma kansa shugaban kasa Muhammad Buhari, an yi tsammanin samun canji daga shugabancinsa, sai ga shi a lokacin sa ake samun rahoton cin hanci da rashawa ta kowanne sashe wanda dan Nijeriya bai taba tunanin haka ba.

dan Malikin Progress, Alhaji Babangida Usman, ya kara da cewa, duk wanda za a kawo domin ya maye gurbin Magu shi din ma bai da tabbas sai dai an gani kawai saboda ba za a yaba masa ba sai in har ya hau ya gama lafiya.

Ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari, da cewa kafin a nada wani ya zama jami’in hukumar ta EFCC tun da waje ne da yake da girma ya dace a sa ido kamata ya yi a tsaya a tantance jajirtacce tsohon maaikaci wanda ba zai bari wani ya yi masa katsalandan a aikin sa ba, ko da shugaban kasa ne, a ba shi iko sosai, idan kuma aka masa shisshigi ya fito ya gayawa duniya jama’a su zama shaida hakan zai sa a samu sauki.

A cewar sa, abin da ya sa ya ce duk wanda za a kawo bai da tabbas kuwa shi ne, saboda duk abin da zai yi daga sama ake ba shi umurni wasu ne suka kawo shi kuma su na neman sai ya biya masu wasu bukatun su a boye idan ba haka ba a yi masa bita-da-kulli za ta sa a cire shi.

Babangida Usman, ya kara da cewa, ai ko cire Magu din ya fara haifar da tone-tone domin ya ce akwai wasu kudi da ya bai wa Mataimakin shugaban kasa shi kuma ya ce bai ba shi ba, ka ga ashe duk wanda za a nada din dan amshin shata ne, sunan dai shi ne shugaban EFCC amma masu ba shi umurnin yadda zai yi suna gefe.

Daganan sai Babangida Usman, ya ce idan ba kashe mu raba ake yi ba, ina dukiyar da aka dinga kwatowa na ‘Yan Nijeriya da gidaje ya aka yi da su, kullum kasa sai kara shiga kuncin talauci da bala’i ake yi, shugaba yana ta yawon kara ciyo wa kasa bashi a duba a gani

Exit mobile version