Bagudu Ya Bukaci ’Yan Nijeriya Su Zama Masu Kishin Kasa A Shafukan Sada Zumunta

Ma'aikata

Daga Umar Faruk,

Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, a jiya ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su yi amfani da hanyoyin sada zumunta don durkusar da Kasa, amma su yi amfani hanyoyin na sada zumunta wurin ganin cewa sun daukaka martabar kasar Ga idon Kasashen duniya.

Gwamnan ya yi wannan rokon ne a lokacin da ya bude wani taron karawa juna sani a kan amfani da kafafen sada zumunta na (social Media) a Birnin-Kebbi.

Wakilin LEADERSHIP A YAU, ya ruwaito rahoton cewa Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu ta jihar ce ta shirya taron bitar ga matasa masu aiki da kafafen sada zumunta a duk fadin Jihar ta hanyar aika labarai.

Haka kuma Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana sabbin kafafen yada labarai na zamani a matsayin wani filin sauyawa nan take, wanda ya sauya fuskar aikin jarida a duniya.

Amma duk da haka ya ce ya kamata ‘yan social media su inganta kyawawan halayen ‘yan Najeriya da irin albarkatun da suke da a cikin kasar, kuma su daina aika labaran da abubuwan da zasu bata sunan kasar Najeriya da al’ummarta.

Gwamnan ya kara da cewa a yayin gudanar da zanga-zangar ta #ndSARS, an yada rahotanni na karya kuma marasa tushe a kafafen sada zumunta da ke nuna kasar Najeriya da al’ummarta na cikin mummunan yanayi.

Bisa ga hakan ya yi kira da a nuna kwarewa da sanin ya kamata a kan batutuwan da suka shafi Najeriya a duk lokacin da za a yada labarai a kafafen sada zumunta.

Tun da farko, Kwamishiniyar Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu, a Jihar Kebbi, Rakiya Tanko-Ayuba ta ce yada bayanai ya kasance wani muhimmin bangare na ilmantarwa da sanar da jama’a abubuwa.

Kwamishiniyar wadda ta samu wakilcin babban sakatare na Din-din-din na ma’aikatar, Alhaji Garba Hamisu, ya jaddada bukatar masu aikin kafafen sada zumunta na social media su kiyaye kyawawan halaye ta hanyar da ta dace da rikon amana.

Haka zalika ta ci gaba da bayyana cewa an shirya taron ne don fadakarwa da sabunta masu halartar taron don basu horo na musumma kan amfani da kafofin sada zumunta na zamani a duk fadin Jihar ta Kebbi.

Bugu da kari Kwamishiniyar ta shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar horassuwar wajen taimakawa gwamnati da al’ummarta wajen yada manufofinta da shirye-shiryenta da kuma arzikin Jihar Kebbi da kasar bakidaya.

Farfesa Nura Ibrahim na Jami’ar Bayero da ke Kano da kuma Abdullah El-Kurebe, gogaggen dan jarida kuma mai rubutun ra’ayin a yanar gizo, sun ce kafofin sada zumunta sun sauya salon rayuwa a halin da ake ciki.

Haka kuma sun bada horo kan batun “Social Media a matsayin wani zamani na ci gaba ta hanyar yada labarai na zamanance da kuma irin ci gaban da aka samu, mutanen biyu sun shawarci masu aiki da shafukan sada zumunta da su tabbatar da inganci da sahihancin labarun kafin sanya wa a shafukan yanar gizo koda yaushe.

Bugu da kari, malaman da ke bada horassuwa sun lura da cewa kafofin sada zumunta suna canza yadda mutane ke rayuwa, gudanar da kasuwanci, aikin noma, kiwon lafiya da duk wasu fannoni na kwazon dan adam, wanda su na ganin sa a matsayin ci gaba ga al’ummar kasar.

Daga karshe Wakilinmu ya ruwaito, cewa bitar wacce ta kasance mai ilimantarwa, fadakarwa da mu’amala ga mahalarta daga ko’ina a cikin jihar.

Exit mobile version