Connect with us

TATTAUNAWA

Bai Kamata ’Yan Kasuwa Su Sa Buri Lokacin Matsala Ba – Ahmad Sanda

Published

on

Masana’antar saye da saidawa ta Rice Deport ta na sayar da nau’in abinci daban-daban na Iya Kudinka Iya Shagalinka, wuri ne wanda ya saba da hada-hadar al’umma, masamman ’yan kasuwa maza da mata, wato Rice Deport Lafia a Jihar Nasarawa. Hakan ya sanya Wakilin LEADERSHIP A YAU, ZUBAIRU M LAWAL, ya ziyarci wannan masana’antar, inda ya gana da daya daga cikin masu tafiyar da harkokin kasuwanci a wannan gurin, AHMAD UMAR SANDA. Ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:

A halin da a ke ciki, cutar Korona ta kawo cikas a harkan tattalin arziki. Ko wannan matsalar ta shafe ku?
Hakika wannan annobar ta Korona ta shafi al’amura da dama na rayuwar al’umma, mu ma ta shafe mu, saboda samun kaya yanzu akwai matsala, ba kamar a baya yadda mu ke saya da yadda mu ke saidawa ba. Yanzu da kudinka ka na neman kaya ba za ka samu ba. Idan ma ka samu, to ba lallai irin wanda ka ke so ba ko na adadin wanda ka ke so.

Tunda harkokin kasuwancinku ya shafi manyan kamfanonin sarafa shinkafa. Da wadanne kamfanoni ku ka fi mu’amala?
Mu na mu’amala da kamfanoni da yawa, amma mun fi ba da karfi a nan kamfanin Holland da ke Rukubi a Doma cikin jihar Nasarawa. Mun fi ba da karfi a gurin biyan su. Kuma mu na mu’amala da kamfanoni da ke jihar Kano da Jihar Kebbi, kamar Labana Watcof da dai sauransu. Mu na mu’amalar kasuwanci da wadanan kamfanonin tunda harkar saye da saidawa ne.

Cutar Korona ta janyo matsalolin hana shiga da fice. Wannan ya shafi harkar da ku ke yi?
Dole ya shafe mu, saboda yadda za a kawo kaya akwai matsala. Yanzu haka mun biya kudin kaya a Kano sama da wata biyu, amma har yanzu babu labari, saboda matsalar cutar Korona ta ya janyo haka. Yakamata a ce yanzu duk kayan da mu ka saya sun shigo ma na, amma saboda rufe kan iyakokin garuruwa ya hana. Akwai kudaden mutane da su ka ba mu su na bukatar kaya, dole ta sanya mu ka dauki wanda ya ke kasa mu ke ba su. Idan kuma bai kai ba, wanda ba zai iya jira ba, mu kan maida ma sa da kudinsa.

Ko akwai kalubalen da ku ke fuskanta tsakaninku da kwastomomin da ku ke ba su kaya?
Yanzu da ya ke babu kayan, ba mu fuskantar kalubale, saboda daidai kudinka, daidai kayanka, saboda yanzu idan ka ba wa wani kaya da ya fi karfin kudinshi, to wajen fitar kudi zai zamo da matsala a yanzu, domin za a rika kawo ma ka matsalolin cewa, komai ya tsaya, harkar sai a hankali da sauransu. To, idan ka na bukatar cigaba da yin mu’amala da mutane lafiya, to ka bai wa mutum kaya na daidai kudinshi.

Mafi yawan lokaci idan a ka shigo watan Ramadan kayayakin abinci su kan kara tsada. Ko me ya ke kawo hakan?
Wannan abin babu abinda za mu ce sai dai mu yi addu’a, saboda a na cikin matsala a kasar nan. Mafi yawan ’yan kasuwa su kan yi amfani da wannan lokacin su biya bukatar kansu. Ko da sun sayi kaya da sauki su na sanya farashi mai yawa a kan kayan, wanda hakan bai dace ba. Wani lokacin na kan ga laifin gwamnati; yakamata a irin wannan lokacin da a ke shiga mawuyacin hali gwamnati ta samar da kayayyaki da zai wadaci ’yan kasuwa ta samar da farashi, ta yadda wani ba zai yarda ya sanya kaya da tsada ba, domin dan ya yi tsada, zai ga na wasu na karewa su na karowa nashi ya na nan.

To, a naku bangaren cikin wannan lokacin na annobar Korona ga kuma Azumi ya shigo, ina batun naku farashin; ya sauka ko ya karu?
Mu kayan da mu ka saya kafin wannan lokacin mun sayar a farashinmu, amma yanzu samun kayan a kamfani ya na wahala. Saboda da yawancin kamfanonin sun tayar da farashin sayar da kaya. Inda dai ka saya haka za ka kintata ka sayar, domin kar ka fadi.

Wane kira ku ke da shi zuwa ga gwamnati wajen taimakon ku a fannin sana’o’in abinci?
Gaskiya yakamata gwamnati ta sanya baki; mu da mu ke harka ta cikin gida, yakamata a ce kayanmu ya fi yawa a kan wadanda za su zo daga waje. Akasarin abincin da a ke sarafawa a nan a na ciyar da mafi yawan ’yan kudancin kasar ne. Su ne su ka fi amfana da kayan da a ke sarafawa a nan fiye da mu na gida. Yakamata a samu fifiko; mu da mu ke jihar. Sannan a kara hannun komai ya zama wadatacce, saboda rashin wadatar kayan ya kan kawo tsadar kayan.

Masu sayan kaya, domin tallafin akwai nasu farashin na daban ne?
Hakika akwai sauki fiye da masu daya biyu, sannan mu kayanmu ya danganta da yadda mu ka sayo, amma mu kan yi sauki.

Wane kira ka ke da shi ga ’yan kasuwa ’yan uwanka dangane da wannan lokacin na annobar cutar Korona da Azumin Ramadan?
Kiran da zan yi wa ’yan kasuwa ’yan uwa na shi ne a ji tsoron Allah a sassuta kuma a tausaya wa jama’a. Na san akwai wadanda su ke amfani da irin wannan lokacin su yi kudi; su na sayen kaya da jimawa su ajiye sai a wannan lokacin su kara farashi. Duk lokacin da a ka samu matsala, sai ka ga kaya ya na tashi. Bai kamata ba. Ko da ka sayi kaya da tsada, yakamata ka sassauta wa al’umma, saboda halin kunci da a ke ciki. Wani zai sanya albarka; yara da mata za su ci su ji dadi su yi godiya. Yakamata a rika kamantawa a tausaya halin da a ke ciki. Idan an bar shi da abin sayen, sai an taimaka ma sa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: