A jiya ne bangarorin biyu na Majalisar Dokokin Nijeriya, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai, su ka koka da yadda harkar jiragen saman kasar ta ke, su na masu yin gargadin cewa, bala’i na iya afkuwa idan har ba a samar da isassun kudade ba. Musamman, ‘yan majalisar sun ce, akalla a na bukatar Naira biliyan 50, don biyan bukatun kamfanonin jiragen sama.
Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Litinin dangane da sakamakon sauraron ra’ayoyin jama’a da a ka gudanar tsakanin ranakun 2 zuwa 4 ga Nuwamba, 2020, a yayin zartar da dokokin zartaswa guda shida, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan sufurin Jiragen Sama, Sanata Smart Adeyemi na APC daga Jihar Kogi ta Yamma, ya yi gardadin cewa akwai hadari a tashin jirgi yanzu a Nijeriya.
Majalisar Dattawan ta ce, ta gano a cikin kwanaki uku na sauraron ba’asin da a ka gabatar a kan kudirin cewa wani bangare na kalubalen da ke fuskantar bangaren jiragen sama shi ne yadda hukumar Kwastam ba ta bi umarnin Majalisar Zartarwa ba, don yin watsi da duk wani nau’i na haraji da ya shafi shigowar kayayyakin gyaran jirage.
Ta kuma kara da cewa, an gano cewa nau’ikan haraji har yanzu suna ci gaba, da kuma rashin bin umarnin majalisar zartarwa kan cire karin kudaden Haraji, BAT, daga safarar jiragen sama, da kuma rashin iyawar masu zirga-zirgar jiragen sama, don samun damar lamuni guda daya, kamar yadda za a iya samu a wasu sassan duniya.
Adeyemi ya bayyana cewa, “Ina so in sanya shi a rubuce cewa akwai hadari a tashin jiragen sama a Nijeriya a yau. Akwai lokutan da wasu jirage ke silalewa daga kan titin su na tashi. Dole ne mu tallafawa masu zirga-zirgar jiragen sama har zuwa lokacin da za mu samu kamfanin jirginmu na kasa. Amma idan muna son ci gaba da aiki kamar yadda yawancin al’ummomin duniya ke yi a yau, ba zai yiwu mu bar su da kansu ba, saboda za su so su kasance cikin kasuwanci da gwagwarmayar neman riba da kari, kuma za su sassauta,” in ji shi.
Tabbas dole ne a yi wani abu don taimaka wa kamfanonin jiragen sama, don su amsa tasirin cutar korona. A matsayinmu na ‘Yan Majalisa, muna ba gwamnatin Nijeriya shawara mai karfi, da ta gudanar da ayyukan haraji ba tare da biyan harajin BAT ba ga dukkan kayayyakin da suka sahfi gyaran jiragen kasuwanci da ake shigo da su Nijeriya. Wannan zai taimaka wajen hanzarta habaka tattalin arziki ko da kuwa ina fuskantar koma bayan tattalin arziki da kasashen duniya ke fuskanta a yau, tare da taimakawa kamfanonin jiragen sama su kasance a kan aiki tare babban burinsu na tabbatar da lafiyar fasinjoji.
Haka zalika, Kwamitin Majalisar Wakilai kan Sufurin Jiragen Sama, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da akalla Naira biliyan 50, a matsayin kudin shiga tsakani da kamfanonin jiragen sama da ke aiki a kasar nan.
Har ila yau, ta kuma bukaci Shugaba Buhari da ya yi hanzarin yin sanarwa da zai ba hukumomin zirga-zirgar jiragen sama damar rike kashi 25 na kudaden shigar su na cikin gida don ci gaban kayayyakin more rayuwa.