Connect with us

BIDIYO

Ban Ji Tsoro Ba Ranar Da A Ka Fara Sa Min Kyamara –Sayyada

Published

on

 

Shahararriyar hazikar jarumar nan da tauraruwarta ta haska a tsangayar Kannywoood wadda kuma ta fara Fim din Hausa tun tana ‘yar shekara shida mai suna Khadija M. Adam da aka fi sani da Sayyada ta ce ba ta tsoro ba a ranar da aka fara haska ta da kyamara a Fim dinta na farko. Sayyada ta bayyana hakan ne cikin tattaunawarsu da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, RABIU ALI INDABAWA, ga yadda hirar ta kasance.

 

Da fari za mu so mu san sunanki da tarihinki a takaice.

To ni dai sunana Khadija M. Adam, amma an fi sani na da suna Sayyada an haife ni ranar biyar ga watan Mayu 2004 a garin Kano cikin Unguwar Sheka Baranda. Na fara karatu tun ina da shekara uku da haihuwa a wata makaranta  mai suna ‘Kids Foundation’ da ke Shagari Ktrs cikin birnin kano.

 

Ki na da shekara nawa ki ka fara fim din Hausa?

Na fara fitowa a Fim tun ina ‘yar shekara shida a duniya.

 

To ko za ki iya tuna Fim din da kika fara fitowa?

Eh, Fim din da na fara fitowa dai shi ne Sayyada

 

Da ma sunanki ne Sayyada ko kuwa dai suna ne aka sa miki na fim din?

Eh, sunana ne da ma Sayyada, saboda sunan kakata ne da haifi babana, shi ne ake kirana da shi.

 

To ke ce ki ka fadawa iyayenki ki na da sha’awar Fim ko su suka yi ra’ayin su kai ki?

To, da ma babana Furodusa ne, kuma dama Fim din na sa ne, an gama zabar dukkan jarumai sai aka rasa wadda za ta hau wannan matsayin na karamar yarinya, sai abin ya fara damunsa, domin an tanadi kowane gurbi, kuma lokaci yana kurewa. To da babata ta ga haka sai ta ce da shi babana, to ga Sayyada me zai hana a gwada ta ai za ta iya? Sai ya ce a gaskiya Sayyada ba za ta iya ba, domin ta yi kankanta kuma ba ta taba yi ba. Sai babata ta ce ka jarraba ta dai ka gani, da ya ga dai ta dage sai ya ce, na amince amma bisa sharadi, idan muka je ta kasa kin ga fa zan yi asara, za ki biya ni kudin da na yi asara? Babata ta ce, eh idan har na ba da matsala za ta biya shi kudin Fim din.

To da ta san an yi wannan yarjejeniya, a kullum idan babana ya fita sai ta dauki karamar bidiyo Kyamara ta rika daukana tana nuna min yadda zan yi. Da haka har na saba da kyamara har kuma na iya magana ba tare da ina kallon kyamara ba, kuma fa duk abin nan da ake yi babana bai sani ba. Ranar fita aiki ta zo jikin babana a sanyaye saboda bai gama gamsuwa da zan iya ba, har aka je wurin da aka fara aiki, ina ganin yadda kowa yake nasa.

To aiki ya zo kaina sai aka yi mamaki, domin an ga babu alamar tsoro a tare da ni, kuma duk abin da ake so na yi shi dai-dai, tun daga wannan Fim din na Sayyada aka ci gaba da sanya ni a finafinai.

 

To yaya kika yi da ‘yan Unguwarku da suka fara ganinki a fim?

A lokacin da tauraruwata ta fara haskawa sai jama’a suka rika yin tururuwa ana zuwa gidanmu kallona masu zuwa ziyara suna masu kawo min kyauta suna bayarwa a a jiye min, a wani lokacin ma idan na ga mutane sun taru a cikin gidanmu sai tsoro ya kamani na gudu daki na buya, ji nake ko wani abu za su yi min. har ta kai ga bana iya fita waje saboda jama’a, kuma duk inda na shiga sai na ji ana ta hira ta, ko wucewa na zo yi sai mutane su yi ta kiran sunana, sai da ta kai zuwa makarantar Allo da Islamiyya, da ta Boko sun gagare ni. To a dai-dai wannan lokaci ne sai mahaifiyata ta rasu, bayan wani lokaci da rasuwarta na ci gaba da Fim, har na shiga makarantar sikandire, a nan ma na samu kyaututtuka a makaranta idan an zo ana irin wannan shirin, ko kuma in mun wakilci makaranta a gasar makarantu na karatu wato ‘Debet’

 

To Sayyada lokacin da aka fara sanya miki Kyamara ba ki ji tsoro ko fargaba kamar yadda sauran jarumai ke ji ba?

A’a ban ji tsoro ba ranar da aka fara sa min kyamara, saboda ai na gaya maka babata ta koya min tun kafin ranar.

 

Da kawayenki suka fara ganin ki a fim me suke cewa da ke?

Murna suka yi.

 

Ba su tsangwame ki sun ce me ya sa kika shiga Fim ba?

Su ma cewa suka yi suna so su shiga Fim din

 

Me ya sa ba ki jawo daya daga cikinsu ba?

To ai ban sani ba ko iyayensu ba za su yarda ba

 

Mahaifinki ya ce a Makarantarku ba a magana da Hausa, yanzu za ki iya yin Fim da turanci?

Gaskiya zan iya ko wane fim da Turanci.

 

To daga lokacin da aka fara sa ki a fim zuwa yanzu kin yi fim kamar nawa?

(Dariya) Gaskiya a yanzu dai ba zai iya fadar adadinsu ba.

 

To a cikin Fina-finan da kika yi, wane fim kika so a zuciyarki?

Na fi son Bararo

 

A wane Fim kika fi shan wahala cikin Fina-finan da kika yi?

A gaskiya na fi shan wahala a cikin Fim din Sayyada.

 

Wane Jarumi ne kika fi son a hada ki fim tare da shi?

Adam A Zango.

 

Wane Jarumi ne ya fi birge ki idan ki na kallon fim dinsa?

Ali Nuhu.

 

A ‘yan shekarun nan an daina ganin fuskarki a Fim wato ba kya fitowa, me ya sa?

Gaskiya saboda ina son na yi karatu ne sosai.

 

Bayan kin kammala karatunki kina so ki ci gaba da fitowa a Fim ko aiki kike son yi?

Aiki na ke son yi.

 

To wane aiki ki ke sha’awa a rayuwarki?

Ina son aikin Likitanci.

 

Yanzu ke nan karatun likitanci ki ke yi ko?

Eh.

 

Ya sunan makarantarku?

Kual Trust, Secondary School

 

Ya sunan Shugaban Makarantar taku?

Sunansa Garba  Ya’u Abubakar.

 

To Sayyada a wannan gudunmawa da kika bayar a Fina-finai, an taba baki irin kyautar nan ta girmamawa? Wato ‘Award’?

Eh an taba ba ni.

 

Kamar guda nawa aka baki?

Guda uku.

 

To a wane Fim da wanne?

Na karba a Fim din Bararo, da Sultan, da kuma Maraici

 

To a ina da ina aka karrama ki?

Akwai kyautar ‘Best kids Actor MTN Arward, sannan akwai ‘Algaita Arward’ inda na samu kyautar ‘Best Up coming actor Arward’ sai kuma kyautar ‘Best Actress a Fim din Bararo.

 

To ko za ki iya tuna sunan kadan daga cikin finafinan da kika yi?

Eh to, akwai Sayyada, da Bararo, da Sultan, da Baban Sadik, da Maraici, sai Fim din Wuta da Aljanna da Mace ta gari, da kuma Abban Siyama, wadannan su kadai zan iya tunawa

 

A karshe wace irin godiya za ki yi ga iyayenki da suke daukar dawaniyarki?

Gaskiya babu abin da zan ce da iyayena illa Allah ya saka masu da aljanna, Allah ya jikan mahaifiyata. Sannan ina godiya ga Malamaina na Arabi da na Boko su ma Allah ya saka masu da alkhairi.

 

Advertisement

labarai