Fadar shugaban kasa ta yi Allah wadai da maganar karya da aka danganta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce ba zai mika mulki ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu ba.
Fadar shugaban kasar ta kuma yi Allah wadai da mutanen da ta kira sarakan yada karya da ke da alhakin ba da labarin.
- Ramadan: Fasto Ya Raba Wa Musulmi Kayan Masarufi A Kaduna
- Shema Ya Bai Wa PDP Sa’o’i 48 Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Masa
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar a ranar Juma’a, ya yi mamakin “ta yaya za ku yi wa wani yakin neman zabe, ku zabe shi sannan ku ce ba za ku mika masa mulki ba?”
Ya ce lamarin da jaridar ‘Sahara Reporters’ suka buga abun takaici ne kasancewar mamallakinsu dan siyasa ne, hasali ma ya sha kaye a zaben shugaban kasa.
A cewar mai magana da yawun shugaban kasar, gwamnatin ta riga ta shirya mika mulki.
“Kwamitin rikon kwarya, wanda ya kunshi wakilan gwamnati mai barin gado da mai jiran gado, na yin taro a kusan kullum suna shirin mika mulki ga gwamnatin Tinubu da Shettima.
“Kwamitoci goma sha uku a matsayin wani bangare na babban kwamitin, sun shirya mika mulki.
“Game da shugaban kasa, al’ummar Daura sun fara shirye-shiryen karbar dansu bayan nasarar mulkin kasar nan na tsawon wa’adi biyu na shekaru takwas. Shi kuma a nasa bangaren, yana da sha’awar komawa gida don jin dadin ritayar da ya yi,” in ji shi.