Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Bangaren Lafiya Da Ilimi Za Su Kara Samun Kudade Daga Kasafin Kudi

Published

on

Majalisar dattawa sun tattauna a kan yin bitan kasafin kudin naira tiriliyan 10.810 na shekarar 2020, inda suka bukaci a kara wa bangaren lafiya da ilimi yawan kudade. ‘Yan majalisan sun kara naira biliyan 301 daga cikin kasafin kudi na wannan shekarar. Sun yi karin kudin ne ta la’akari da bukatar da mutane suke da shi a wasu fannuka, domin gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata a cikin wannan kasa. ‘Yan majalisar sun kara wa hukumar bayar da ilimin bai daya kudade wanda suka kai na naira biliyan 1.709 daga cikin naira biliyan 51.120. haka kuma, ‘yan majalisar sun kara biliyan 25.560 a bannin lafiya daga cikin naira biliyan 897.

Bitan kasafin kudin na shekarar 2020, ya kasance kamar haka,  an kara wa bangaren gudanar da ayyuka kudi na naira tiriliyan 2.230, wanda ya karu zuwa naira tiriliyon 4.928. Bitan kasafin wanda shugaban kasa Buhari ya sake aika wa majalisa da shi ya nuna cewa, bashin da za a biya ya kai na naira tiriliyan 2.95, sannan aka cire naira biliyan 500 na magance cutar Korona. An gabatar da kasafin kudin inda za a dunga sayar da dala daya na Amurka a kan naira 360, sannan za a dunga hako danyen mai ganga miliyan 1.8 a kowacce rana, inda kowacce gangan danyen mai take a kan dala 25, yayin da ‘yan majalisa suka kara zuwa dala 28 a kan kowacce gangan mai.

Da ya ke gabatar da sake bitan kasafin kudin, shugaban kwamitin kudade na majalisa, Solomon Adeola ya bayyana cewa, an kara farashin mai danyen mai daga dala 25 zuwa dala 28 ga kowacce ganga na danyen mai, inda za a samu raran naira biliyan biyar.

A cewarsa, cikin wannan biliyan biyar da za a samu a matsayin kari ga farashin danyen mai, an kara wa ma’aikatan raya yankin Niger Delta naira biliyan 1.746 a cikin naira biliyan 44.200, yayin da aka kara wa ayyukan bunkasa yankin Arewa maso Gabas naira miliyan 816 daga cikin naira biliyan 20.944.

A cikin bayaninsa bayan an kammala bitan kasafin kudin na shekarar 2020, shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya bukaci dukkan kwamitin da ke cikin zauran majalisa da su yi amfani da ikonsu na saka ido a kan yadda za a aiwatar da wannan kasafin kudi.

“Za mu tabbatar mun saka ido wajen yadda za a kashe kudaden kasafin kudin shekarar 2020, domin mu tabbatar da an kashe kudaden ta yadda ya kamata wajen amfanar da ‘yan Nijerya,” in ji shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: