ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Barau Ya Gargaɗi Gwamna Abba Kan Siyasantar Da Batun Tsaro A Kano

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago
Barau

LABARAI MASU NASABA

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

A wani sabon martani da ya fito daga ofishinsa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi kira ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya daina siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa abin da ake buƙata shi ne aikin gwamnati mai ma’ana don magance matsalolin da suke addabar jihar. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta zargi Sanata Barau da yin magana da ka iya kawo cikas ga ƙoƙarin tsaro, zargi da ya ce ba shi da tushe balle makama.

Sanata Barau, ta bakin mai magana da yawunsa Ismail Mudashir, ya ƙalubalanci gwamnati da ta fito fili ta nuna bidiyon da ake cewa ya yi magana da ke tayar da tarzoma. Ya jaddada cewa a dukkan lokuta yana aiki tare da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki wajen magance barazanar ƴan fashi da hare-haren da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano da ƙasar baki ɗaya. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta karkatar da hankalinta daga gudanar da mulki yadda ya kamata zuwa yaɗa kalaman da ba zasuyi  amfani ga al’umma.

  • Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
  • ‘Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Kashe Ɗan Wasan Barau FC A Katsina

Sanata Barau ya ce rashin daidaito a gwamnati ya sanya Kano ta rasa matsayinta na zama sahun gaba wajen ci gaba a Nijeriya, inda ya buƙaci Gwamna Abba ya tashi tsaye wajen mayar da jihar kan tafarkin ci gaba. Ya kuma yi nuni da gudunmawar da ya bayar a fannin tsaro, ciki har da samar da motocin aiki, da babura ga jami’an tsaro, da gina ofisoshin ƴansanda, da kuma taimakawa hukumomin DSS, da NSCDC, da Immigration ta hanyar kawo cibiyoyin horo a Gwarzo, da Kabo da Bichi.

ADVERTISEMENT

Ya ƙara da cewa fitilun tituna na Sola da ya saka a ƙananan hukumomin Kano Arewa da sauran yankuna ya taimaka wajen inganta aikin ƴan sintiri da rage laifuka. A cewarsa, irin waɗannan aiyuka su ne ya kamata gwamnatin jihar ta na yi, maimakon neman ɓata masa suna. Ya buƙaci gwamnatin Kano da ta yi koyi da irin wannan jajircewa wajen tabbatar da tsaro da ingantaccen mulki ga al’ummar jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Siyasa

Cikin Sauƙi Na Yanke Shawarar Komawa APC – Gwamna Fubara

December 18, 2025
Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe
Siyasa

Ba Zan Taɓa Komawa Jam’iyyar APC Ba — Abaribe

December 16, 2025
El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027
Siyasa

El-Rufai Ya Ƙaryata Rahoton Goyon Bayan Yanki Ko Wani Mutum A Zaɓen 2027

December 15, 2025
Next Post
Cutar Sikila Ba Mutuwa Ba Ce – Ƙwararru

Cutar Sikila Ba Mutuwa Ba Ce - Ƙwararru

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.