Connect with us

RIGAR 'YANCI

Batancin ‘Social Media’ Ba Zai Karya Min Gwiwa Ba – Matar Gwamnan Bauchi

Published

on

Uwargidan gwamnan jihar Bauchi, Dakta A’isha Bala Muhammad ta yi tir, tare da karyata shaci-fadin wasu kafofin watsa labaran zumunta na zamani na cewar, ta yi rabon ruwan sha na ledar ‘Pure Water’ wa al’ummar garin Futuk ta cikin karamar hukumar Alkaleri ta jihar.

Wannan shagube dai da kafofin sada zumunta na zamani (Social Media) suka tallatar na kyautar ruwan sha na leda kadai daga cikin daukacin kayayyakin tallafi da uwargidan gwamnan ta rabawa mabukata a garin Futuk, an yi ne da zummar aibunta wannan kyakkyawar aniya nata.

Dr. A’isha Mohammed dai, da take karyata wannan shaci-fadi ta bakin babbar sakatariyar watsa labaran ta, Hajiya Murjanatu Musa Maidawa, ta bayyana cewer, kayayyaki da da ta rabawa al’ummar garin Futuk sun hada da Injuna na sarrafa abincin sufageti, fulawa ta sarrafa abinci, da kuma makudan kudade a matsayin wani jari na dogaro da kai.

Uwargidan gwamnan ta kuma fadi cewar, tunda farko sai da gidauniyar ta, ta horas da mata da matasa guda dari biyu da hamsin (250) kan sana’o’i dabam-dabam da suka hada da dinke-dinken tufafin sanyawa, markada kayayyakin abinci da Injuna, hadi da na’urorin yin kitso na wa mata, bisa cancantar horo da mabukata na garin Futuk suka samu.

Uwargidan gwamna ta bayyana cewar, gidauniyarta ta ‘Almuhibbah’ a shekaru goma sha uku (13) da kafuwarta bata taba gudanar da horaswa ko raba kayayyakin tallafi na jari wa gungun mutane, ba tare da ta tuntube su kan ire-iren sana’o’i da su ke bukata ba.

“A matsayin ta na uwa wacce ke fafi-tikar tallafawa rayuwar marasa karfi matasa da mata, wannan batanci na kafofin sada zumunta na zamani ba zasu karya mata gwuiwa kan aniyar ta na tallafawa mabukata ba”, Inji sanarwar.

A’isha ta ce, da farko dai bata yi niyyar mayar da martani ba kan wannan shagube, amma sai ta yi la’akari da yin hakan ita ce hanya mafi dacewa, “domin ance yaki dan zambo ne, don haka abu ne mai sauki shaguben ya rinjayi wasu masu raunin fahimtar lamura, su amince da wannan batanci, duk da cewar, galibin mata da matasa a wannan jiha ta Bauchi suna da yakini na ire-iren gudummawar Gidauniyar Almuhibbah na tallafawa al’umma.”

Uwargidan gwamnan ta kuma yi al’ajabin yadda wadannan kafofi na sadarwar zumunta suka ki kulawa da sauran kayayyakin tallafi data rabawa jama’ar garin Futuk, sai suka zabi tallata ruwan sha na leda a matsayi na cewar shine kadai kayan tallafin nata, domin su cimma biyan bukatar su ta batanci, “Wannan sam ba adalci bane; kuma hakan ba zai taimaki al’umma da komai ba,” a cewarta.

Sanarwar, ta kuma yi la’akari da cewar, ire-iren wadannan shagube na batanci da wadannan kafofin yanar gizo na sada zumunta ke wallafawa, yana daya daga cikin tanade-tanaden sun a hanawa uwargidan gwamna aikata alheri, hadi da manufar su ta dakushe aniyar gwamnatin Kauran Bauchi na samar da romon dimokaradiyya wa wadanda suka zabe ta.

Sanarwar ta Murjanatu Maidawa ta nemi masu irin wannan dabi’ar da su sauya domin aza tubulin gina al’umma a kowani lokaci.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: