Batun Kiwon Lafiya Na Bai-daya A Nijeriya…

Kiwon lafiya na daya daga cikin muhimman al’amura na rayuwar al’umma da ya kamata shugabanni a dukkanin matakai su ba shi kyakkyawan kulawa, saboda alakarsa ba ga jindadin rayuwa ba kawai, har ma da dorewar rayuwar baki daya.

Gwamnatocin kasashen da suka samu cigaba a duniya ba su yin sako-sako da batun kiwon lafiya wanda hakan ya sa kasashe masu tasowa suke kokarin koyi da su. Nijeriya kasarmu ta gado, ita ma ta yunkuro domin ganin ta fitar da jaki daga duma kan abin da ya shafi kiwon lafiyar al’ummarta inda ta zage damtse wajen ganin ta cimma burinta na tabbatar da kiwon lafiya bai-daya.

Sai dai wannan ba zai kai ga gaci ba, face an yi kyawawan tsare-tsare da za su kasance ba na jeka-na-yi-ka ba, kuma a tabbatar da an bi matakan da suka dace wurin aiwatarwa. Hatta su kansu masana da aka sallama musu a kan tsara manufofin aiwatarwa sun sha tofa albarkacin bakinsu game da hanyoyin da za a bi wurin aiwatar da shirin kiwon lafiyan na bai-daya.

Shi dai wannan shirin na kiwon lafiya bai-daya kamar yadda Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana, yana nufin wani tsari ne da kowa da kowa a cikin al’umma zai samu ingantaccen kula da lafiyar da yake bukata ba tare da ya sha wahala ko yin mikar da ta wuce kima ta kudi a kan bukatarsa ba. Tsari ne da yake kunshe da yadda za a warkar da mara lafiya, ko yin rigakafi ko kuma inganta koshin lafiya ga jama’a cikin sauki. Ma’ana idan aka samu nasarar aiwatar da shirin a Nijeriya, matsalolin da suka addabi musamman talakawa idan sun je asibiti irin su ‘likita ba zai taba mara lafiya ba har sai an biya wasu makudan kudi’, da ‘rashin kayan aiki’, ko kumma tsauwala wa masu jinya, duk za a yi bankwana da su.

Nijeriya kasarmu ta gado, Allah ya albarkace ta da fitar da duk wani abu da za a yi mai nagarta da inganci, amma inda gizo-ke-saka shi ne wurin aiwatarwa. A ra’ayinmu wannan ne babban dabaibayin da ya sharke shirin kiwon lafiya na bai-daya da ake son aiwatarwa a kasar.

Tun a shekaru uku da suka gabata, an amince da kudirin shirin ya zama doka wanda abin da ya rage kawai shi ne aiwatarwa. Masu ruwa da tsaki a sha’anin sun yi imanin cewa da zarar an aiwatar da shirin, sashen kiwon lafiya na kasar zai yi gyaruwar da ba a taba gani ba. Amma tun daga lokacin da aka rattaba wa kudirin shirin hannu ya zama doka, gwamnatin da ta tsara shirin, ta kuma bi matakan da suka dace wurin samun halascinsa ta kasa ware kudin da ake bukata domin cikakkiyar aiwatarwa don haka ta cimma ruwa.

Idan za mu iya tunawa, tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya rattaba wa kudirin dokar hannu ya zama doka ne tun a watan Disambar shekarar 2014, bayan ya shafe shekara shida ana tafka mahawara a kansa tare da matsin lamba daga kungiyoyin cigaban al’umma da suka yi yakinin cewa shirin zai cike katon gibin da aka dade ana fama da shi a sashen kiwon lafiyar kasar.

Shirin kiwon lafiyan na bai-daya ya yi tanade-tanade masu alfanu da za su bunkasa sha’anin kiwon lafiya a ko wane mataki. Dokar shirin ta yi tanadin cewa gwamnatin tarayya ce za ta samar da kudin aiwatar da shi tare da wani kebantaccen kaso daga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi.

Sannan a sashe na farko, karamin sashe na shida, an jadda muhimmancin aiwatar da dokar domin baiwa jama’a damar samun ingantaccen kiwon lafiya. Dokar ta kuma yi bayani dalla-dalla kan kason da za a ware na sayen magunguna, kayan aiki na dakunan bincike da sufuri, da daukan ma’aikata da kuma tanadin shirin ko-ta-kwana. Mata masu juna biyu, da yara ‘yan kasa da shekara biyar da haihuwa, tsofaffi da kuma nakasassu duk kyauta za a rika kula da lafiyarsu, kana an amince a rika karbar wadanda hatsari ya rutsa da su kai-tsaye a asibitocin gwamnatin da masu zaman kansu.

Bugu da kari, dokar ta yi tanadin da za a inganta cibiyoyin kula da lafiya, sannan ta dakile dabi’ar kwashe makudan kudi daga aljihun gwamnati da nufin biya wa ma’aikata kudin magani a kasashen waje da kuma takaita zuwa wajen neman magani a tsakanin ma’aikatan gwamnati wadda ya zama abin gasa da ake rige-rigen yi tare da kashe milyoyin dalolin harajin da ‘yan kasa ke biya a kan hakan.

Wannan duka abin kunya ne ga Nijeriya tun da ba ta rasa arzikin da za ta gyara sashenta na kiwon lafiya kamar yadda sauran kasashe sa’o’inta ke yi ba.

Tsarin kiwon lafiyar kasar ya zama abin tausayi musamman a yankunan karkara da babu isasshen magani ballantana kwararren likita, babu asibiti ballantana dakunan gwaje-gwajen cututtuka. Har ila yau, duk da shirin kiwon lafiya tun daga matakin farko, da shirin inshorar kiwon lafiya da ake aiwatarwa a kasar, yanayin kiwon lafiyar jama’a bai kai matakin da ake fatan gani ba.

Saboda haka muna kira ga gwamnatin tarayya ta muhimmanta batun aiwatar da shirin na kiwon lafiya bai-daya, kamar yadda aka rattaba wa kudirin shirin hannu ya zama doka, domin samun sahihi kuma ingantaccen kiwon lafiya a tsakanin al’ummar kasar nan.

Exit mobile version