Dan wasan kasar Poland, Robert Lewandowski da Manuel Neuer da kuma Thomas Müller suna daga cikin ‘yan wasa 23 da Bayern Munich ta ce za su buga mata kofin Zakarun nahiyoyi na FIFA Club World Cup.
A kasar katar za’a buga gasar da ya kamata a yi a shekara ta 2020, wadda aka soke zuwa bana, sakamakon kalubalen da cutar korona da ta haddasa wadda da farko ma cewa akayi ba za’a buga gasar ba kafin daga baya hukumar kwallon kafa ta duniya ta canja shawara.
kungiyar Bayern Munchen, mai kofin Champions League da na Bundesliga da ta lashe a bara na fatan cin kofin zakarun nahiyoyin duniya da za a fara daga ranar 4 ga watan nan zuwa 11 ga watan Fabrairu.
Idan har ta yi nasara zai zama kofi na shida da ta lashe a watanni 12 sai dai a baya kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce ke da wannan bajintar a nahiyar Turai a shekarar 2009 a lokacin da kungiyar take sharafinta.
Kawo yanzu Bayern Munich tana da kofin Bundesliga da na DFB Cup da na UEFA Champions League da UEFA Super Cup da kuma DFL Supercup da ta mallaka a kakar bara duka a karkashin mai koyarwa Hansi Flick.
Da yake ita ce mai rike da kofin Champions League na Turai za ta fafata ne a karawar daf da karshe da duk wadda ta yi nasara tsakanin Al-Duhail ta Dubai ko kuma Al Ahly mai rike da kofin nahiyar Afirka ranar 8 ga watan Fabrairu.
Da zarar Bayern Munich ta kai karawar karshe, za ta fafata da duk wadda ta yi nasara tsakanin Palmeiras ko kuma Tigres/Ulsan Hyundai ranar 11 ga watan Fabrairu a wasan da za’a fafata a kasar katar.
Wannan kofin zai zama na hudu na duniya idan Bayern ta lashe shi, bayan da ta ci Intercontinental Cup a shekarar 1976 da kuma 2001 wanda hakan yasa kungiyar ta shiga sahun irinsu Real Madrid da AC Milan da Barcelona da kuma Manchester United wajen lashe kofunan.
‘Yan wasa 23 da za su buga wa Bayern Munich Fifa World Club Cup:
Masu tsaron raga: Manuel Neuer da Aledander Nubel da kuma Ron-Thorben Hoffmann.
Masu tsaron baya: Niklas Sule da Benjamin Pabard da Jabi Martinez da Jerome Boateng da Bouna Sarr da Lucas Hernandez da kuma Dabid Alaba.
Masu buga tsakiya: Joshua Kimmich da Leon Goretzka da Marc Roca da Corentin Tolisso da Kingsley Coman da kuma Jamal Musiala.
Masu cin kwallaye: Serge Gnabry da Robert Lewandowski da Leroy Sane da Douglas Costa da Eric Madim Choupo-Moting da Alphonso Dabies da kuma Thomas Muller.