Aƙalla mutane 30 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun mutu a wani mummunan hari da kungiyar ‘yan sa kai ta cikin gari ta yi a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru, jihar Zamfara.
Kamar yadda wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana daga bayanan sirri, harin ya faru ne a kimanin karfe 2 na rana a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu.
- Mun Rage Tasirin ‘Yan Bindiga A Kebbi Da Zamfara – Sojoji
- Nasara A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda: Tattalin Arziƙin Jihar Zamfara Na Ƙara Haɓaka – Gwamna Lawal
An ce ‘yan fashin suna kan hanyarsu ta kai hari wani kauye kusa da su, amma sai suka yi kicibus da ‘yan sa kai na yankin, Yansakai, wadanda suka mamaye wajen shahararren birnin. A cikin artabun da ya biyo baya, an samu mutuwar waɗanda ake zargin su da kai hare-hare.
Haka kuma, an samu motocin haya guda 16 da ake zargin ‘yan fashin sun yi amfani da su yayin kai hare-haren, kamar yadda Makama ya shaida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp